Shahararrun ýan ƙkwallon Duniya
musulmai masu zuwa aikin Hajji
akai akai.
Kusan za’a iya cewa babu wasan motsa jiki
a duniya da aka fi kallo kamar kwallon
kafa, wato wasan tamola sakamakon da
wuya kaje wani gari ko kauye baka tarar
da al’ummar wurin suna buga ta ba.
Yan kwallon sune wadanda aka fi sanya
ma idanu a yayin buga kwallon fiye da
kowa, don haka muka kawo muku jerin
sunyen wasu shahararrun yan wasan
kwallon kafa Musulmai dake zuwa aikin
hajji akai akai don bautar Allah.
1. Paul Pogba
(Pogba)
Idan ka biye ta sunan dan wasan, sai ka
zata ba musulmi bane, sai dai Paul
Pogba cikakken musulmi ne, kuma har
ya samu damar sauke farali ta hanyar
zuwa hajji a rayuwarsa, ban da Umara
da ya sha zuwa.
Pogba
2. Emmanuel Adebayor
(Adebayor)
An haifi Adebayor, tsohon dan wasan
Arsenal a shekarar 1984, ranar 26 ga
watan Feburairu, kuma asalinsa
mabiyin addinin Kirista ne tare da
iyayensa da danginsa.
Shahararrun ýan ƙwallon Duniya musulmai masu
zuwa aikin Hajji akai akai
Amma a kwanan nan ne Adebayor ya
canza addini, ya musulunta, kuma ya
bada hujjar musuluntar tasa. Bayan
karbar musuluncin nasa ne, sai
Adebayor ya kai ziyara dakin Allah
domin aikin Hajji a kasar Saudi Arabia.
3. Mesut Ozil
(Ozil)
Masana kwallon kafa sun tabbatar
Mesut Ozil na cikin gagga gaggan yan
kwallon duniya, wanda ko a kasar sa ta
haihuwa Jamus, an dade ba’a samu
kamar sa ba. Sai shima Ozil musulmi
ne, kuma yana gudanar da aikin Hajji a
duk shekara.
4. Abou Diaby
{Abou Diaby}
Haka zalika tsohon dan wasan Arsenal
Abou Diaby wanda yanzu ya koma buga
wasa a kungiyar Marseille shima
musulmi ne, kuma yayi aikin Hajji ba
sau daya ba, ba sau biyu ba.
5. Nicolas Anelka
(Anelka)
Tsohon dan wasan Arsenal da Chelsea,
Nicolas Anelka musulmin kirki ne sosai,
kuma ya jajje kasa mai tsarki don
gudanar da aikin Hajji.
No comments:
Write Comments