Thursday

Home An sake gano sabbin duniyoyi 7 masu kama da tamu duniyar.



Hukumar Binciken Kan Sararin Samaniya ta Amurka NASA ta bayyana cewa, an ganO yiwuwar samun ruwa da kuma iya rayuwa a duniyoyin da suke sama.

Hukumar Binciken Kan Sararin Samaniya ta Amurka NASA ta bayyana cewa, an gano yiwuwar samun ruwa da kuma iya rayuwa a duniyoyin da suke sama.
A yayin binciken an yi amfani da na'urar NASA mai karfi ta Spitzer wadda ake bincike kan sararin samaniya da ita.

Wadannan sabbin duniyoyi da aka gano suna da nisani tafiyar haske ta tsawon shekaru 40 kuma suna kusa da tauraron da ake kira Trappist-1.
An gano cewa, daga cikn sabbin duniyoyin 7 uku na kama da tamu duniyar kuma an gano yiwuwar akwai abubuwa da ke nuna an rayu a cikinsu.
Hakan dai na nufin za a iya zama a cikinsu matukar aka tabbatar da wanzuwar ruwa.

Masana sun ce, gano wadannan duniyoyi na da matukar muhimmanci game da binciken da ake yi kan yin rayuwa a wajen duniyarmu.
No comments:
Write Comments