Tun tafiyar shugaba Muhammadu Buhari
kawo yanzu mukaddashin shugaban kasar
Yemi Osinbajo ya dauki matakai da ayyuka
da dama a kasar.
Yanzu haka dai Farfesa Osinbajo ke rike
da Najeriya ya kuma yi ayyuka tafiyar
shugaba Buhari na a-zo-a-gani. Kadan
daga ciki su ne sauyi da aka gani a
tsare-tsaren harkar kudin kasar daga
CBN. Farfesa Osinbajo kuma ya shiga
lungunan Neja-Delta domin kwantar da
rikicin da ke Yankin.
Mukaddashin shugaban kasa Farfesa
Yemi Osinbajo ya saki kudin wasu
manyan kwangiloli a Kaduna da Legas
wancan makon bayan taron Majalisar
FEC. Haka kuma Shugaban rikon
kwaryar ya ci burin gyara tattalin
arzikin Najeriya ta hanyar saukake
harkar kasuwanci a kasar cikin watanni
biyu.
Gawurtattun abubuwan da Osinbajo yayi tafiyar
Buhari
Tun hawan sa dai ya nada Kwamiti
domin ya ji dalilin da ya sa farashin
abinci ya tashi a Najeriya. Farfesa
Osinbajo ya kuma gana da shugabannin
Majalisa ba sau daya ba, ba sau biyu ba
a game da harkar kasafin kudin
wannan shekarar.
Osinbajo ya kuma rattaba hannu a wasu
kudirori da Majalisar ta aiko masa
yayin da kuma yayi mursisi yayi watsi
da wasu kudirorin tare da bayyana
dalilan sa. Har a kasar waje dai ana ta
kawo ziyara ga shugaban kasar na
rikon karya inda shi ma ya taka har
kasar Gambia wajen nadin sabon
shugaba Adama Barrow.
No comments:
Write Comments