Sunday

Home › › Manyan ‘Yan siyasar Arewa sun ce sai sun gindayawa Osinbajo sharudda in har yanaso su mara masa baya.


Manyan ‘Yan siyasar Arewa sun gindayawa Osinbajo sharudda

‘Yan Arewa sun gindayawa Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo wasu sharudda – Idan dai har za su goyi bayan Osinbajo sai ya cika wadannan sharudda – Da alamu siyasar Najeriya za ta canza zani Manyan ‘Yan siyasar Arewa sun gindayawa Osinbajo sharudda Manyan ‘Yan Siyasar Arewa sun gindawa Mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo wasu sharudda idan har yana so su goya masa baya a tafiyar. Da alamu dai siyasar Najeriya na iya canza zani a cikin kwanakin nan bayan rashin lafiyar shugaba Buhari.

Ana tunanin idan har shugaba Buhari ya gaza, za a nada Mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo SAN ya cigaba a matsayin shugaban kasa. To sai dai ‘Yan Arewan sun bada sharuddan goyawa Mataimakin baya idan hakan ta kama.

SHARUDDAN DAI SUNE



  • Dole ya nemo mataimaki Musulmi dan Arewa.


  • Sannan kuma ba zai tsaya takara ba a zabe mai zuwa.


  • Haka kuma dai Osinbajo ba zai taba mutanen shugaba Buhari ba.


  • Shekaran jiya Mukaddashin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo SAN ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya zuwa Jihar Ribas da kuma Jihar Bayelsa a Yankin Neja-Delta domin ganin an kawo karshen rikicin yankin. Ana nan dai ana jiran tsammanin dawowan shugaban kasar.

    A biyo mu a shafin mu na facebook @facebook/HAUSAPOST28
    No comments:
    Write Comments