Wasu ma’aurata da ke zaune a birnin Leicester, Leicestershire, UK sun ga wani abun al’ajabi.
Anisa Jussab na kokarin soya wani abu wa mijinta Farid sai ta lura da wani zane a cikin kwan da ta saya a kasuwa. Da ta duba jikin kwan sosai, sai taga rubutun sunan Allah.
Tace: “Wannan ba abinda wani zai iya rubutawa bane akan kwai. Wannan abin na bayyana kuma na ji irin wannan na faruwa a kan bishiyoyi da girgije. Wannan wata ay ace kuma sako ga dukkan musulmai domin gafartawa juna…”
Farid yace: “ Lokacin da ta dauki kwan ta ji alamun rubutu a hanuna sai ta tsira ido, kawai sai ga sunan Allah. Ina kwance sai ta zo da gudu ta tashe ni.
Akwai hasken ranan sosai kuma ina iya gani sosai. Sai da tsiga jikina ya tashi. Abin yayi matukar bamu mamaki. Da wuri na je na fada limamin masallaci Imamu Bukhari sai yace mu ci kwan.”
No comments:
Write Comments