Friday

Home Masu Zanga-Zanga Sun Afkawa Kamfanin MTN
Farmakin ramuwa kan MTN



A Najeriya masu zanga-zanga sun auka wa ofishin wayar salaula na MTN da ke Abuja don ramuwa bisa kashe 'yan Najeriya da aka yi a kasar Afirka ta Kudu yayin rikicin kyamar baki.

Kakakin MTN a Najeriya ya fadawa manema labarai cewa, mutanen suna zanga-zanga ne kan hallaka 'yan Najeriya wanda zauna gari banza masu gyamar baki suka yi a Afirka ta Kudu.

Farmakin an kai shi ne a ofishin MTN da ke Abuja wanda, shi ne babban cibiyar sayarda layin salula na kamfanin a kasashen Yammacin Afirka da kuma ofishin hulda da jama'a na MTN.

A cewar kakakin na MTN, wadanda suka kai farmakin sun lalata na'u'rorin kamfanin, kana suka sace wayoyin salula na kwastomini da ke cikin ofishin a lokacin da masu boren suka shiga.
No comments:
Write Comments