Friday

Home Abubuwa sun fara saituwa :Naira ta kara Daraja.
Naira tayi tashin da ba ta taba yin irin sa
ba
A cikin ‘yan kwanakin nan dai Naira tana
kara mikewa
Ba mamaki sabon tsarin CBN ne ya kawo
haka


Ayyiruri: Naira tayi sama.


Da alamu hakar babban bankin
Najeriya na CBN za ta ci wa ruwa don
kuwa har abubuwa sun fara yin kyau.
Kwanan nan ne dai babban bankin
kasar watau CBN ya sauya tsare-tsaren
sa na harkar kudin kasar.


Makon jiya dai sai da Nairar tayi irin
dukan kasar da ba ta taba yi ba, don
kuwa an wayi gari an samu Dalar
Amurka tana kan Naira 520, Tun da ake
ba a taba samun lokacin da Naira ta
fadi war-was kamar haka ba.


Yanzu haka dai ana sayar da Dalar
Amurka a kan N470 wanda an samu
ragin kusan N50 kenan cikin ‘yan
kwanaki biyu. Babu dai lokacin da
Naira tayi irin wannan yunkuri.
Kwanan nan ne babban bankin kasar
watau CBN ya saki dalolin miliyoyi ga
bankuna, hakan ya kawo sa’ida wajen
samun dalar.

A haka kuma kudin kasar wajen
Najeriya ya kara tashi zuwa kusan Dala
Biliyan 30. Farashin man Najeriya dai
ya karu don haka abubuwa suke zuwa
da dan sauki cikin kwanakin nan.
No comments:
Write Comments