Cutar daji na daya daga cikin cututtukan da ke sa mutum ya rasa ransa farad-daya musamman idan an dade a na fama da shi ajiki ba sani ba ko kuma ba ayi gaggawar daukan mataki akai ba.
Ga wasu hanyoyi 6 da zaka bi domin gujewa kamuwa daga cuttar daji wato Kansa ko kuma samun sauki akai.
1- Turmeric: Wata sinadari ce wanda ya yi kama da citta sannan kuma yana daya daga cikin sinadarorin da ake amfani da su wajen sarrafa garin curry. Bincike ya nuna cewa ita Turmeric na da karfin kare mutum daga kamuwa da cutar daji kowace iri sannan kuma ana iya amfani da shi wurin magance cutar idan an kamu da ita.
2. Cin kayan itatuwa: idan aka hada kayan itatuwa kamar lemu, kankana, abarba, tufa, ‘ya’yan inabi da kuma sauransu wuri daya aka sha wato ko a nika ko kuma a yanyanka yana taimakawa wajen rage cutar daji a jikin mutum sanna kuma yana iya kare mutun daga kamuwa da cutar idan dai ana sha kullum.
3. Jijiyan itacen kwakwa wanda ya kai shekara 7: idan aka dafa jijiyar aka sha ruwan, ana samun sauki daga cutar daji.
4. Yawan amfani da roba ko leda a zuba abinci kaman alalen leda da akeyi, zuba tuwo a leda ko kuma a sha shayi a kofin roba na kawo cutar daji.
5. Shan ganyen shayin da ake kira green tea na kare mutum daga kamuwa da cutar sannan kuma ana iya amfani da shi domin rege cutar idan an kamu.
6. Shan kayan zaki da ake siyarwa a gwan-gwani ko kuma abinci a gwan-gwani na kawo cutar daji. Amma idan aka rage amfani da su ana iya samun kariya daga cutar kuma hakan zai rage yaduwar cutar a jikin mutum idan an kamu.
No comments:
Write Comments