
Majalisar dattawa ta kafa kwamitin mutane
biyar domin gudanar da bincike akan zargin
karya dokar aiki da zargin kashe wasu kudade
ba tare da izini ba wanda shugaban hukumar
inshorar kiwon lafiya ta kasa NHIS Usman Yusuf
ya yi.

Da yake tofa albarkacin bakinsa akan maganar
Sanata Kabiru Marafa ya ce kamata ya yi a
bincike aiyukkan da shugaban hukumar inshoran
ke yi duk da cewa shugaban kasa Muhammadu
Buhari ne ya na da shi a watan Yulin shekarar da
ya gabata.
A bayanin da ya yi yace Yusuf ya kashe wasu
kudade ba tare da ya nemi cikakken izini ba daga
ministan kiwon lafiya Isaac Adewole.
Ana zargin Yusuf da yin watanda da kudaden da
suka kai naira miliyan 960 wanda hakan ya wuce
kudaden da doka ta bashi ikon kashewa ba tare
da amincewar ministan kiwon lafiya.
Bayan haka sanata Marafa ya zargi Yusuf da
daukar ma’aikata ta hanyoyin da bai dace ba
sannan ya canza ma wasu ma’aikatan wajen
aikin bayan basu cancanci haka ba kumaya kara
ma wasu ma’aikatan da ba su dace ba girma a
hukumar.
A wani bincike da wannan gidan jarida yayi akan
wannan badakalar, ta gano cewa Yusuf yana
ikirari da cewa babu wanda ya isa ya muzguna
masa domin shi dan gatan Buhari ne.
Bayan haka kuma angano cewa a dalilin haka
Usman Yusuf baya kula ministan kiwon lafiya
sannan baya masa ganin ya isa ya bukaci wani
abu game da hukumarsa a wajen ministan.
No comments:
Write Comments