Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu
Sunusi II ya gargadi shugaban kasa Muhammadu
Buhari da yayi taka tsantsan da fadawansa na
fadar gwamnati, don kuwa tamkar masu amshin
shata suke.
Sarkin yayi wannan gargadi ne a ranar Alhamis
23 ga watan Maris a taron tunawa da babban
lauyan Kehinde Sofola a jihar Legas, inda yace
yan amshin shata sune asalin makiyan shugaban
kasa Muhammadu Buhari, kuma idan bai bi a
hankali dasu ba, zasu lalata duk wani kokarin
dayake yi.
Sarki ya shawarci Buhari da kada ya dinga
kyamar masu sukar gwamnatinsa “Ina tausayin
masu rike da madafan iko, saboda a koda yaushe
zagaye suke da makiya” , Sarki yace ya shugaba
Buhari na bukatan mutanen da zasu dinga fada
masa gaskiya komai dacinta.
Sunusi yace dalilin daya sa ya fallasa badakalar
sama da dala biliyan 20 a zamanin gwamnatin
tsohon shugaban kasa Goodluck shine saboda
baya tsoron barin kujerarsa, saboda ya san ba zai
dawwama a kujerar dindindin ba.
Sarki yace wasu mutane suna tsoron fada ma
shuwagabanni gaskiya ne saboda gudun kada a
sallame su daga aiki, “duk mutanen da ake tsoron fada ma gaskiya suna ina ne yanzu? Don haka
wadanda suke kan mulki suma su tuna mulki mai
wucewa ne.” inji shi
Mai martaba ya cigaba da fadin cewa baya
ruduwa idan fadawa suna fada masa cewa zai
dawwama a kan mulki, don haka ne ma baya
tuntubarsu dangane da muhimman shawarwari,
sa’annan dalilin daya sa ya daina sukar shugaba
Jonathan shine saboda ya bar mulki, don kuwa
idan na kan mulki ne zaka fada masa gaskiya.
“idan kana son zama dan kasa na gari, toh ka fada
ma gwamnati mai ci gaskiya”.
Dayake bada labarin yadda ya bar kujeran
gwamnan CBN, Sunusi yace “Dole dai wata rana in
bar kujerar gwamnan CBN, zan iya mutuwa, wa’adin
mulki na ka iya karewa, ko kuma a tsige ni, bani
da iko kan wannan. Don haka ban yi mamakin
sallama tab a, na san a rina, saboda an taba
umarta ta da inyi murabus, amma naki ya.
“Amsa daya na basu, kace in yi murabus saboda
na fada maka an saci kudi, sai dai ka fara fada ma
ministan tayi ritaya.
“Mutane sun manta cewa wannan gwamnan ko
shugaban kasa da kake jin tsoron fada ma gaskiya
zai bar kujerarsa wata rana, abinda kawai za’a iya
tunaka da shi a kai, shine yadda ka tafiyar da
rayuwarka a lokacin da kake raye.” Inji mai matarba Sarki
No comments:
Write Comments