Thursday

Home Iran ce Kadai Kasar Da 'Yan ta'adda Ba Su Sami Nasarar Kai Hari A cikinta ba.


Iran ce Kadai Kasar Da 'Yan ta'adda Ba Su Sami Nasarar Kai Hari A cikinta ba.

Ministan harkokin tsaro na Iran ya ce; Bisa Taimakon Allah, Iran ce Kadai Kasar da 'yan ta'adda su ka kasa kai hare-haren ta'addanci a cikinta.

Ministan harkokin tsaro na Iran ya ce; Bisa Taimakon Allah, Iran ce Kadai Kasar da 'yan ta'adda su ka kasa kai hare-haren ta'addanci a cikinta.

Hujjatul-Islam Sayyid Alawi, ya fada a jiya da dare cewa; Makiya daga ko'ina a duniya sun yi kokarin yin kutse a cikin Iran,amma bisa taimakon Allah da ludufinsa, an dakile dukkanin makarkashiyar da su ka kitsa.

Sayyid Alawi Mahmudi ya yi ishara da jawabin sabuwar shekara na jagoran juyin musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamnei da a ciki ya ambaci cewa al'ummar Iran sun rayu cikin aminci a shekarar 1395 hijira shamshiyya da ta gabata.

ministan harkokin tsaron na Iran din ya ci gaba da cewa; Tsaro, ginshiki ne na abubuwa da dama da su ka hada da al'adu da tattalin arziki da harkokin addini.
No comments:
Write Comments