Thursday

Home Azabarwar Da Al'ummar Musulmin Rohinga Na Kasar Myanmar suke fuskanta. (1)



Azabar Al'ummar Musulmin Rohinga Na Kasar Myanmar.

Al'ummar Rohinga da a wannan lokacin suna shan wahala a hannun masu tsaurin ra'ayin addini na mabiya addinin Bhudda a kasar Myanmar, a hakikanin gaskiya suna cikin 'yan asalin wannan kasar da ake nuna cewa su baki ne.

Ita dai kasar Myanmar tana a kudu maso gabacin nahiyar Asiya ne. Kuma tana cikin daya daga kasashe mafi talauci a yankin kudu maso gabacin Asiyar. Sai dai a girman kasa ita ce ta biyu a cikin yankin.

Gundumar Rakhine, wacce a baya ake kiranta da Arkan tana a gabar ruwa ta yammacin kasar Myanmar. Yanki ne wanda ya yi iyaka da Kasar Sin ta arewa sannan kuma iyaka da ruwa, Begaladesh ta yamma har ta tsawon kilo mita 275. Girman yankin na Rakhane ya kai kilo mita 37000. Iyakokin ruwa da yankin da ya ke da shi, ya saukake shigar addinin musulunci a cikinsa a karshen karni na 7.

Al'ummar Rohinga su ne mazaunan asali na wannan yanki, daruruwan shekaru a baya. Kuma tarihinsu yana da tushe da wannan kasar da su ke rayuwa akanta.
Sun karbi addinin musulunci, kuma a halin da ake ciki a yanzu kawo 70 % na mazauna yankin musulmi ne.

Marubuta tarihin shigar musulunci yankin, suna ambatar cewa; tun a karnin farko na bayyanar musulunci ya isa wannan yankin. Al'ummun kasashen Iran da kuma larabawa da su ke tafiye-tafiye da a ruwa, sun rika watsa sakon addinin musulunci.. Yankin Arkhane kuwa shi ne inda su ka rika ratsawa domin isa cikin yankuna kudancin Asiya da zummar isar da sakon addinin musulunci. A can ne kuma su ke yada zango domin hutawa. Don haka yankin farko da ya zama na musulmi a kusa da Sin, shi ne wannan yankin na Arkhane.

'Yan kasuwar kasar Sin, a wancan zamanin, sun yi rubuce-rubuce da su ka rika ambaton; mazaunin Iraniyawa da ke kan iyakar Myanmar ta yanzu da kuma gundumar Yunin, da ke kudu maso yammacin kasar ta Sin.

Wata mahangar ta tarihi kuma tana bayyana mutanen Rohinga da cewa; su mutane ne musulmi da su ke da tushe na Ariyanci. Kuma an yi wani zamani da su ke da tsarin sarauta nasu a karkashin mulkkin Sulaiman Sha wanda ya kasance daga 1430 zuwa 1784. Sarautar tasu ta rayu na tsawon shekaru 350.

Bayan Sarkin Sulaiman a matsayin sarki na farko, Rohinga sun yi sarakuna musulmi 48 bayansa. An yi kudaden da aka rubuta Kalmar shahada a jikinsu.
Baya ga wanann, yankin ya shahara da harkar kasuwanci saboda iyakokin ruwa da ya ke da su. Tafikin Kaladan, ce mafi girma a gundumar, domin yana kwararowa ne daga kan duwatsun Himilaya, Da akwai dazuka masu duhu da su ka lulluba yankin na tsawon kaso 70%.

Har zuwa shekarar 1774 musulmin Rohinga da su ke rayuwa a wannan yankin ba su da wata matsala. Amma daga lokacin da wani mabiyin addinin Bhudda mai suna; Bhuddapaya, wanda ya sami karfin iko.

Musulmin Rohinga sun kasance masu rayuwa da makwabtansu da ba musulmi ba cikin zaman lafiya da lumana. Amma wancan mutumin mai suna Bhuddah –Paya ya dora harsashin kiyayya da musulmi. Lokacin da ya isa wajen da musulmi su ke ya rusa tsarinsu na sharia da musulunci. Daga wancan loakcin ne kuma sabani ya fara kunno kai a tsakanin musulmi da yan bhuddah. Har zuwa shekarar 1824 da Ingila ta mamaye kasar, ta hade ta da Idiya
Wasu daga cikin musulmin kasar Indiya sun yo hijira su ka shiga cikin yankin na Rohinga. Domin kuwa yankin ya zama wata cibiya ta kasuwanci da kuma rayuwa mai kyau, musamman ga musulmi.

Wasu mutanen daga kasar Bangaladesh sun rika fitowa daga kasar tasu suna zuwa yankin na Arkhane saboda kaucewa hare-haren 'yan Bhudda a yankunansu. Wani dalilin na yin hijira zuwa yankin shi ne matsin lambar da 'yan mulkin mallakar Ingila su ka rika yi musu. Saboda samun sauki sun rika ficewa daga cikin yankunan nasu suna zuwa yankin.

Gwamnatin kasar Myanmar cikin ganganci ta rika bayyana musulmin yankin da cewa dukkaninsu 'yan gudun hijira ne da su ka shiga kasar daga Bangaladesh, saboda haka su ke hana su hakkin zama yan kasa.

A cikin shekarar 1937, Birtaniya wacce ta ke son aiwatar da manufofinta na mulkin mallaka, ta cire kasar ta Myanmar wacce a wancan lokacin ake kira da Burma, daga jikin kasar Indiya. Yankin na Arkhane ya kasance a karkashin wannan sabuwar kasar da Birntaniyan ta kirkira.

Al'ummar musulmin wannan kasa, su ne na farkon wadanda su ka fara kalubalantar mulkin mallaka. Sun kuwa yi tsayin daka wajen fada da danniya da zaluncin 'yan mulkin mallakar na Birtaniya.

Saboda haka da dama daga cikin wahalhalun da musulmin Rohinga su ke sha a yanzu, yana a matsayin ramuwar gayya ce saboda matsayarsu ta fada da 'yan mulkin mallaka. Hakan kuma yana faruwa ne a karkashin siyasar nan da makirci da aka san Birtaniya da ita, ta raba kan mutane domin a ji dadin mulkinsu.

""Ku kasance tãre damu don jin kashi na (2)""

A matsayinsu na musulmai "yan uwanmu muna Addu'ar Allah ya kubutar DA su daga sharrin azzalumai.

Ameen.
No comments:
Write Comments