‘Yan Siyasan da ke shirin tsayawa takara a zaben 2015.
A wani nazari da Jaridar Daily Trust tayi mun fara kawo maku jerin ‘yan siyasan da ke iya tsayawa takarar shugabancin kasar a zabe mai zuwa na 2019. Mun kawo kadan daga ciki akwai Bola Tinubu, Yemi Osinbajo dsr. Yanzu haka ga cigaba nan:
1-Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban kasar bai taba boye muradin sa na shugabancin Najeriya ba an kuma sha bugawa da shi da dadewa a Jam’iyyu dabam-dabam. Har yanzu dai daga kalaman Alhaji Atiku za a gane inda yake shirin kadawa sai dai daga cikin masu yi wa Atiku adawa akwai tsohon shugaban kasa kuma mai gidan sa Olusgeun Obasanjo.
2-Bukola Saraki
Saraki na iya tsayawa takara a zabe mai zuwa don kuwa yayi yumkurin hakan a wancan karo karkashin APC kafin ya janye. Bukola na rike da Majalisa gam a hannun sa kuma da yake matashi ne har yanzu akwai yiwuwar yayi abin kirki. Bukola dai tsohon Gwamnan Jihar Kwara ne da ke tsakiyar kasar wannan ma wani abu ne.
3-Rabiu Kwankwaso
Sanata Kwankwaso tsohon Gwamnan Jihar Kano ne wanda kuma yake wakiltar Kano ta tsakiya a Majalisar Dattawa, Kwankwaso rikakken dan siyasa ne. Injiniya Kwankwaso yayi abin a zo-a gani a Kano lokacin yana Gwamna ya kuma bada tsoro lokacin da ya tsaya takarar a wancan zaben. Bayan shugaba Buhari, Kwankwaso mutum ne mai dinbin Jama’a a Najeriya.
4-Sule Lamido
Sule Lamido yana cikin masu shirin tsayawa takara a PDP. Lamido dai gawurtaccen dan siyasa ne don kuwa da su aka kafa Jam’iyyar PDP. Tuni dai Sule tsohon Gwamnan Jihar Jigawa ya bayyana shirin sa na tsayawa takara. Ko zai kai labari? Oho.
[KU CIGABA DA KASANCEWA DA MU, Za mu cigaba da kawo maku sauran jerin nan gaba]
No comments:
Write Comments