Kwakwalwar wanda ya mutu na cigaba da aiki bayan mintuna 10 da mutuwarsa
Wana gangamin likitoci sunga abin al’ajabin da basu taba gani ba.
Malaman Kimiya sun samu hujjan cewa akwai rayuwa bayan mutuwa
Wata gangamin likitocin kasar Kanada sun gudanar da wata bahasi inda kwakwalwan mamaci ke cigaba da aiki bayan minti 10 da mutuwarsa.
Masu bincike na jami’ar Ontario sun kasance suna lura da zuciya da kwakwalen mutane 4 da ke jinya a asibiti bayan an kashe na’urar da ke rike da su.
KU KARANTA: Wani Kwararren Likita Daga London, Yã gãno Cutar Dake Damun Shugaba Buhari.
Shin menene alakan wannan rayuwan barzahu? Wannan bincike zai bada masa.
Abinda aka sani a likitance shine idan zuciyan mutum ya tsaya, to shikenan komai na shi yak are, amma abinda ya basu mamaki shine bayan zuciyar daya daga cikinsu ya tsaya, kwakwalwan na cigaba da aiki. Wannan na faruwa ne kawai idan mutum na bacci.
Wannan hujja ne cewa ashe ko bayan mutum yam utu, zai iya rayuwa.
No comments:
Write Comments