Babbar Akantar jihar Kano Aisha Muhammad Bello ta bayyana cewa biyan albashin ma'aikatan jihar a makare ya zo karshe sakamakon kammala tantance ma'aikatan jihar.
Mai rike da mukamin accounter janar Aisha Muhammadu Bello ta bayyana dalilin da ake samun tsaiko wajen biyan albashin ma'aikata a kan kari a jihar.
Matasalar biyan albashi a makare a Kano ta zo karshe - Babbar Akanta janarkantar jihar Kano
Babbar Akantar jihar Kano Aisha Muhammad Bello ta bayyana cewa biyan albashin ma'aikatan jihar a makare ya zo karshe sakamakon kammala tantance ma'aikatan jihar.
A wata hira babban akantar ta yi da yi da Jaridar NAIJ.COM a ranar 12 ga watan Maris a Kano, ta ce, kason da gwamnatin Kano ke samu na tafiya kachokam ga biyan albashin ma'aikata.
Wanda ya haka ya tilastawa gwamna Abdullahi Umar Ganduje soma tantance ma'aikata don sanin yawansu da kuma hakikanin yawan albashi da alawus-alawus da kuma fansho da yakamata su karba a duk wata.
KARANTA WANNAN :- Wasu Malaman Kimiya sun samu hujjar cewa akwai rayuwa bayan mutuwa.
Gwamnatin ta kuma dukufa wajen tantance ma'aikatan jihar masu karbar albashi da 'yan fasho ta hanyar daukar hotunansu da kuma zanen yatsun hannusu wanda hakan ya kawo tsaiko wajen biyan albashin watannin Disamba da na Janairu.
Kasancewa a yanzu gwamnatin ta na gab da kammala wannan aiki ta gano bakin zaren, a inda ta biya albashin watan Fabararu a kan lokaci,
Kuma a cewar Babban Akantar, za ta biya na watan Maris a kan kari da kuma na sauranta watanni masu zuwa da yaradar Allah.
Hajiya Aisha ta kuma bayyana wadanda ba su samu albashin na su ba da cewa, wandanda ke da matsalar tantancewa ne ko kuma a bankunansu a inda ake aika musu albashin.
Ma'aikatan jihar dai sun dade suna korafi dangane da rashin biyansu a kan kari wanda 'yan adawar siyasa suka danganta da rashin kudi.
Ga hoton bidiyon zanga-zangar goyon bayan Buhari da aka yi a jihar a kwanakin baya
No comments:
Write Comments