Tsohon shugaban mulkin soja, janar Ibrahim Badamasi Babangida ya bayyana haka, inda yace jam’iyar ta PDP zata iya mulkin Najeriya na tsawon shekaru 60, matukar za a sasanta rikicin cikin gida da yake damun jam’iyar.
Babangida ya bayyana hakane yau a gidansa dake Mina can jihar Neja, lokacin da yake karbar bakuncin shugabannin jam’iyar, yace PDP ce jam’iya daya tilo da jama’a suka sani, suka mora, kuma suka rugumeta hannu biyu.
Yakuma jaddada goyon bayansa kan komawa tsarin jam’iyu biyu inda yace hakan zai kara bunkasa dimakwaradiyya.
KARANTA WANNAN :- Tsakanin Hameed Ali da Sanatoci: Ba’a nada ni shugaban Kwastam don saka Uniform ba.
Anasa jawabin shugaban tawagar Farfesa. Jerry Gana, ya shawarci jam’iya mai mulki ta APC da ta kyale yan adawa su bayyana ra’ayinsu.
Jam’iyar PDP dai ta dade tana fama da rikicin shugabanci a matakin tarayya, inda bangarori biyu suke ikirarin shugabancin jam’iyar, kwanan baya ne dai wata kotu dake fatakwal ta bayyana bangaren sanata Ali Modu sharif a matsayin hallatacen shugaban jam’iyar.
No comments:
Write Comments