An samu rarrabuwar kawuna
tsakanin magoya bayan Osinbajo
da Buhari.

Yanzu haka takaddama ta kaure a Najeriya
tsakanin magoya bayan shugaban kasar
Muhammadu Buhari da magoya bayan
Mukaddashin shugaban Yemi Osibanjo, kan
rikon kwaryar da aka bashi sakamakon
rashin lafiyar Buhari.
tsakanin magoya bayan Osinbajo
da Buhari.
Yanzu haka takaddama ta kaure a Najeriya
tsakanin magoya bayan shugaban kasar
Muhammadu Buhari da magoya bayan
Mukaddashin shugaban Yemi Osibanjo, kan
rikon kwaryar da aka bashi sakamakon
rashin lafiyar Buhari.
Yayin da wasu ke yabawa mukaddashin
shugaban kasar Osibanjo kan matakan
da ya ke dauka cikin kankanin lokaci,
wasu na cewa ai duk wani mataki da ya
ke dauka, umurni ne daga mai gidan sa
Buhari.
Wannan ya sa mai taimakawa
shugaban kasar Babafemi Ojudu ya ce
duk wani mataki da Osibanjo ke dauka
sai ya tuntubi Buhari kafin ya aikata.
Duk wannan na zuwa ne a daidai
lokacin da shugaba Buhari ke ci gaba da
jinya a Birnin Landan na Britaniya da
ya kwashi kusan wata daya.
No comments:
Write Comments