Shugaban Muhammadu Buhari zai dawo Yau, Juma’a. Wannan ya bayyana ne ta shafin sada zumunta da ra’ayin mai Magana da yawun shugaba kasa, Mr. Femi Adesina.
Karanta jawabin:
Ana sa ran dawowar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, A Yau Juma’a, 10 ga watan Maris 2017.
Shugaban kasan ya bar kasan ne ranan 19 ga watan Junairu, 2017 domin hutu sannan ya ga likita. An jinkirta ranan dawowarsa ne bisa ga shawaran likitoci na cewa ya sake hutawa.
Shugaba Buhari yana mika godiyarsa ga "yan Najeriya da kewaye wadanda suka yi masa addu’a da kuma mika gaisuwarsu.”
SANARWA DAGA FEMI ADESINA
Mai Magana da yawun shugaban kasa.
March 9, 2017.
No comments:
Write Comments