Friday

Home Zaben 2019 : zai Gudana ne ta hanyar computer da kuma na'urar tantance masu kada kuri'a : majalissa




Majalisar dattawan Najeriya ta yi wa dokokin zaben kasar na 2010 wasu gyare-gyare, inda a cikin dokar ta shigar da batun cewa za a gudanar da zabukan kasar nan gaba ta hanyar amfani da kwamfuta da kuma na'urar tantance katin zabe.

Majalisar ta gabatar da sabbin dokokin zaben ne a wani zama da ta yi ranar Alhamis, wanda shugabanta Sanata Bukola Saraki ya jagoranta.
'Yan majalisar sun kuma amince da wani mataki na rarraba sakamakon zabe zuwa cibiyoyin zabe ta kwamfuta.

Akwai yiwuwar wannan doka za ta sauya tsarin gudanar da zabe baki daya a Najeriya nan gaba.
Majalisar dattawan ta ce, ''Kwaskwarimar da aka yi wa dokar ya fito karara ya bai wa hukumar zaben damar gudanar da zabe ta wannan sabon tsari, sannan kuma ya ba ta ikon amfani da wasu hanyoyin idan waccar hanyar ta kasa yiwuwa."
Haka kuma, majalisar ta kayyade kudin sayen fom din shiga takara na shugaban kasa a kan naira miliyan 10, da na gwamna a kan naira miliyan biyar, da na majalisar dattawa a kan naira miliyan biyu, da kuma na majalisar wakilai a kan naira miliyan daya.
Majalisar ta kuma sakala wani sabon karamin sashe a karkashin sashe na 19 na Dokar Zaben, wanda ya wajabta wa INEC kafe kundin rajistar masu zabe na ko wacce karamar hukuma ko mazabar kansila a ko wacce cibiyar zabe da ma a shafinta na intanet.

A zabukan shekarar 2015 ma an yi amfani da na'urar tantance katin zabe a Najeriya, inda 'yan kasar da dama ke ganin ta taka muhimmiyar rawa wajen rage irin magudin da ake ganin ana tafkawa a harkar zabe, duk kuwa da irin matsalolin da aka dinga fuskanta wajen amfani da na'urar a lokacin.
No comments:
Write Comments