Saturday

Home Yadda Na auri yan matan Chibok 2 : A cewar Kwamandan yan ta'addan Boko Haram


- An ruwaito cewa wanda aka kama shugaban
yan ta’addan ya tona asirin a kwanakin da suka
gabata


Joseph David

A hira ta musamman da kuma bincike fiye da
makonni bakwai a wasu yankunan jihar
Borno, babban dan jaridar The Nation mai
suna Olatunji Ololade ya bayyana abubuwa
da suka faru

Tsohon kwamandan mayakan Boko Haram ya
bayyana yadda ya tilasta biyu daga acikin
yan matan Chibok sama da 250 da wata
kungiya ta garkuwa da su a watan Afirilu,
2014.

Wasu daga cikin yan matan Chibok da an ceto daga
hannun yan Boko Haram
Shugaban wata kungiya mai suna Joseph
David, banasare ne kafin ya zama dan
ta’addan. Yace ya amfana da yan matan
Chibok biyu domin shi, kwamandan Boko
Haram ne.

Amma, abun ban dariya ne maganar David,
wani dan asalin garin Mubi dake jihar
Adamawa, saboda yan Boko Haram sun
garkuwa da shi kuma a yayinda ya cika dan
shekara 22 da haihuwa, kamar yadda
majiyar mu ta samu rahoton.

Kwamandan ya jaddada da shi dan polytechnic
Adamawa ne dake garin Yola a lokaci an
garkuwa da shi.

A yanzu, ya zama mai shekaru 25. Yana cikin
hannun jami’an tsaro bayan rundunar sojin
kasa ta kama shi.

Kafin a kamashi, yana karba albashin
N500,000 a wata-wata. Don wannan
gagarumin albashi, yayi aure daga cikin yan
matan Chibok bayan matarshi farkon
Faridah.

David yana jin dadi acikin dajin Sambisa
kafin shugaban gaba daya yan Boko Haram
Abubakar Shekau ya fushi da shi.
No comments:
Write Comments