Tuesday

Home › › Boko Haram ta kashe mutane kasuwar Konduga : Maiduguri

Boko Haram ta kashe mutane 27 a Konduga da ke jihar Maiduguri/ BOKO HARAM.

Rahotanni daga birnin Maiduguri na jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa, kungiyar Boko Harm ta kaddamar da hare-haren kunar bakin wake a karamar hukumar Konduga, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 27.

Maharan su tayar da bama-bamai guda biyu a wata kasuwa da ke karamar hukumar kuma a dai dai lokacin da jama’a ke tsaka da cin kasuwancinsu a yammacin wannan Litinin da ta wuce.

Bam na uku ya tashi ne a sansanin ‘yan gudun hijira da ke garin na Kondugan kamar yadda Yusuf ya shaida mana.

Ana fargabar cewa, adadin wadanda suka mutu ka iya karuwa saboda munin farmakin.
Garin Konduga mai tazarar kilomita 30 daga birnin Maiduguri na daya daga cikin yankunan jihar Borno da suka fi fama da hare-haren Boko Haram, lamarin da ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.

SABODA ALLAH YANXU HAKA ZA'A SAWA WANNAN MUTUMIN SHEKAU IDO A NIGERIA, YABI YA ZAME MANA CIWON IDO.

ANCE MANA BURUTAI DA IYALANSA SUN KOMA MAIDUGURI AMMA SUNA INA AKA TASHI HAR BOM UKU HABA JAMA'A GASKIYA YA KAMATA "YAN AREWA MU SAKE TUNANI..........

kalle shi lokacin da yasake sakin faifan bidiyi a wannan litinin din data wuce.

No comments:
Write Comments