Saturday

Home Yanzu Yanzu : AFRICMIL ta maka Buhari kotu kan cire $496m don sayen jirgin Tucano
Cibiyar nan da ke fafutukar ilimantar da jama'a dangane da tattara bayanai da watsa labarai ta Afrika, AFRICMIL, wacce kuma cibiya ce mai zaman kanta, ta shigar da kara akan shugaban kasa Muhammadu Buhari, bisa sayen jiragen yakin sama kirar Tucano har guda 12 da kudinsu ya kai $496m ba tare da izinin majalisun tarayya na kasa ba.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cire wadannan kudade ne daga asusun rarar danyen mai (ECA).

Karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1179/2018 na da shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, 'yan majalisun dattijan, kakain majalisar wakilai ta tarayya, Rt. Hon. Yakubu Dogara, da kuma yan majalisun wakilai na tarayyar, a matsayin shaidu kan wannan karar.





Cibiyar AFRICMIL ta ce ta shigar da wannan karar ne la'akari da karamin sashe na 3 da na 4 na babban sashe na 80 da ke cikin kundin tsarin mulkin kasa na 1999 (kamar yadda aka yi masa gyaran fuska).

Cibiyar ta ce tana kalubalantar shugaban kasa Muhammadu Buhari, a matsayinta na kashin kanta, akan dalilin sa na cire kudin jama'a don sayen jiragen ba tare da samun izinin yin hakan daga hadakar majalisun wakilai na kasar ba.
"Babu wasu kudade da aka amince a fitar dasu daga asusun gwamnati, baicin kudaden haraji na gwamnatin tarayyar, har sai idan cire wadannan kudade ya samu amincewa daga majalisun wakilai na tarayyar kasar."
Daga baya ne dai shugaban kasa Buhari ya bukaci yan majalisun da su sanya wadannan kudade da ya cire a cikin kasafin 2018.
Masu shigar da karar, sun bukaci kotu ta gano: "Ko shi wanda ake karar (Buhari) na da karfin ikon cire $462,000,000.000 (Dala miliyan dari hudu da sittin da biyu) ko kuma wasu kudade daga asusun gwamnati don sayen jiragen yakin sama, kirar Super Tucano, akan koma wanne dalili ne ba tare da samun izinin cire kudin daga majalisun tarayyar kasar ba, dub da sashe na 81, 82 da kuma 83 na kundin tsarin mulkin Nigeria na 1999 (kamar yadda aka sake masa fasali)."

SOURCE : Haualegit.ng
No comments:
Write Comments