Tuesday

Home › › Dakurun soji sun ceto mutane 1,127 daga hannun Boko Haram - Hukumar Sojin Najeriya
- Dakarun Sojojin Najeriya sunyi nasarar ceto farar hula 1,127 daga hannun mayakan Boko Haram a yayin da suka kai musu samame a kauyuka da dama da ke kan iyakan Najeriya da Kamaru
- Sojojin Najeriya sunyi hadin gwiwa da Sojojin kasar Kamaru wajen fatatakar yan ta'addan daga garuruwa kamar Kusha-Kucha, Surdewala, Alkanerik, Magdewerne da sauran su
- Sojojin sunyi nasarar kwato makamai daban-daban da halaka yan ta'ada sama da 33 duk dai a yunkurin nasu na murkushe ragowar yan ta'addan da ke buya a dajin Sambisa da yankin tafkin Chadi
Dakarun Sojin Najeriya sunyi nasarar ceto mutane 1,127 daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram daga wurare daban-daban a yankin tafkin Chadi da kuma dajin Sambisa. Wadanda aka ceto din sun hada da maza, mata da kuma yara kanana.
Sanarwan ta fito daga bakin mai magana da yuwun dakarun 'Operation Lafiya Dole, Onyeama Nwachukwu a ranar Talata.

Labari mai dadi: Dakurun soji sun ceto mutum 1,127 daga hannun Boko Haram - Hukumar Sojin Najeriya
Sanarwan ta bayyana cewa dakarun Sojin Najeriyan sun kai samame garuruwa da yawa tare da yin kacha-kacha ta mabuyar mayakan Boko Haram da dama.

A dai cikin sanarwan, Nwachukwu ya bayyana cewa a jiya 26 ga watan Fabrairu, Dakarun na Sojin Najeriya tare da hadin gwiwar Sojojin kasar Kamaru sun kai samame a garuruwan Kusha-Kucha, Surdewala, Alkanerik, Magdewerne da kuma Mayen duk a kan iyakan Najeriya da Kamaru inda sojojin sukayi nasarar kashe yan ta'adda 33 kuma suka kwace bindigogi guda 15.
Rundunar kuma sun lalata bama-bamai guda hudu tare da kwace babura da keke mallakan yan ta'adan. Sojojin sun ceto mutane 603 daga kuma an tafi da su zuwa Bama da Pulka don ayi musu tambayoyi kafin a mika su ga sansanin yan gudun hijira.
A wata samamen kuma, sojojin sunyi nasarar kai samame a kauyukan Bokko, Daushe, Gava, Miyanti da Wudala inda nan ma suka tsiratar da mutane da dama kuma suka kwace makamai, ababen hawa da kayan abinci.
Idan mai karatu bai manta ba, NAIJ.com kawo rahoton inda Sojojin Najeriya suka kai wani samame a dajin Sambisa kuma sukayi nasarar kashe yan ta'addan da dama tare da kama wani babban kwamandan kungiyar.

SOURCE @HAUSA.NAIJA.NG
No comments:
Write Comments