Friday

Home › › Hukuncin kotu: Ka salami Magu yanzu ko kuma mu dau mataki – Majalisar dattawa zuwa ga Buhari
Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci shugaba
Muhammadu Buhari ya salami mukaddashin shugaban
hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin
kasa zagon kasa EFCC, Ibrahim Magu, da wuri-wuri.
magu, ibrahim magu, Buhari 2019
Majalisar ta bayyana cewa idan har shugaba Buhari bai
koreshi ba, ba zasu sake sauraron wani bukatar
tabbatarwa daga fadar shugaban kasa, yadda ba zatayi
amai ta lashe a kan al’amarin Magu ba.

Game da majalisar dattawa, za’a cigaba da wannan
takaddama har sai an tabbatar karfinsu na tabbatar da
shugabannin hukumomi kamar da dokarsu a majalisa ta
tanada duk da cewa babu a cikin kundin tsarin mulkin
Najeriya.

Kakakin majalisan dattawa, Sabi Abdullahi, ya bayyana
wannan ne a ranan Alhamis yayinda yake fashin bakin
aka abubuwan da suka tattari rashin tabbatar da muradun
fadan shugaban kasa.

Jaridar NAIJ.com ta bada rahoto jiya cewa kotun Jastin
Dan Tsoho ta yanke shari’ar cewa majalisar dattawa na da
hurumin rashin tabbatar da Ibrahim Magu a matsayin
shugaban hukumar EFCC.

SOURCE ; HAUSA-NAIJA.NG
No comments:
Write Comments