Wani mutum mai suna Siraj mai shekaru 32,
ya watsa ma matarsa mai suna Fara mai
shekaru 25, guba wato acid tana cikin bacci
saboda ta haifar masa diya mace shi kuma
namiji yakeso.
Tayi mummunar kuna a sakamakon gubar da
Siraj, wanda aka fi sani da Bhura ya zuba
mata tana cikin bacci, a garin Moradabad
kusa da New Delhi, a ranar Litinin kamar
yadda jaridar Daily Mail ta ruwaito.
Yace bata biyashi ladan sadakinta daya biya
ba tunda bata haifa masa namiji ba. Mutumin
ya ja mata munanan raunuka a jiki wanda
yasa jami’an ‘yan Sanda suka shiga
farautarsa.
An hanzarta kai Farah asibitin karkara
sokamakon mummunan halin da ya jefata,
inda ta samu kuna a Fuska, hannuwa, da
kuma ciki.
Ma'aauratan dai sunyi shekara takwas tare
kuma suna da yara biyu duk mata.
SOURCE @HAUSA.NAIJA.NG

No comments:
Write Comments