Saturday

Home An yi mummunan hatsarin mota tsakanin motar Dangote da ta fasinjoji
A yammacin yau, Asabar, ne aka samu afkuwar wani mummunan hatsarin mota a kan jihar Nasarawa zuwa garin Jos.

Hatsarin ya afku ne a garin Akwanga tsakanin kwalejin Ilimi da makarantar sakandire ta Mada Hill.
Rahotanni sun bayyana cewar motar fasinja ta jihar Gombe ce tayi taho mu gama da motar kamfanin Dangote kuma nan take mutane 8 suka mutu. Wani shaidar gani da ido y ace mai yiwuwa adadin mutanen da suka mutu ya karu, musamman ganin yadda wasu fasinjojin ke cikin mawuyacin hali. Duba hotunan;

Motar fasinjoji da hatsari ya ritsa da ita.


No comments:
Write Comments