Sunday

Home Ku Duba: Hotunan Da PDP Ta Saki A Matsayin Shaidar Magudi.
Jam’iyyar PDP tayi watsi da sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar na zaben gwamnan jihar Ekiti da aka yi jiya. A sakamakon da INEC ta fitar, dan takarar jam’iyyar APC, Kayode Fayemi, ya sami nasara a kan dan takarar PDP, Farfesa Kolapo Olusola.
Da sanyin safiyar yau, Lahadi, ne hukumar INEC ta sanar da cewar Fayemi na APC ya samu nasara a kananan hukumomi 11 a cikin 16 dake jihar ta Ekiti. Fayemi ya samu jimillar kuri’u 197,459 yayinda Kolapo ya samu kuri’u 178,121. Saidai a jawabin da ta fitar ta bakin kakakinta, Kola Ologbondian, ta bayyana cewar an yi masu fashin zabe da tsakar rana tare da yin watsi da sakamakon zaben gabadayansa. 
Cewar PDP, sakamakon zaben da suke da shi daga mazabun jihar, ya nuna sune keda mafi rinjayen kuri’un da aka kada a zaben amma aka yi amfani da karfin gwamnati da jami’an tsaro aka canja sakamakon zaben. 
Acikin wasu jerin sakonni da Jamiyyar PDP ta fitar a shafinta dake dandalin sada zumunta na Tuwita ta saki wasu hotuna(kamar yadda ku ka gani a sama) da tayi ikirarin cewar na irin magudin da aka tafka mata ne a zaben na jiya.


 

No comments:
Write Comments