Tsohon Gwamna Attahiru Bafarawa yayi jawabi a wajen taron Jam’iyyar PDP inda ake shirin fitar da ‘Dan takarar Shugaban kasa a Garin Fatakwal. Bafarawa yace har ya gama Gwamna bai karbi albashi ba Jihar Sokoto. Haka kuma Alhaji Attahiru Bafarawa ya bayyana cewa a lokacin da yayi mulki, a gidan sa ya zauna ba gidan Gwamnati ba. Sai dai duk da wannan ‘Dan takaran na PDP yace bai nemi alawus daga aljihun Gwamnati ba.
Attahiru Bafarawa da sauran ‘Yan takaran PDP sun yi jawabi takaitacce a wajen babban taron Jam’iyyar da ake yi. Bafarawa wanda yayi Gwamna tsakanin 1999 zuwa 2007 ya dade kwarai da gaske a harkar siyasar Najeriya.

No comments:
Write Comments