Yanzu-yanzu: Yan sanda sun watsa wa Bukola Saraki, Sule Lamido, Tambuwal barkonon tsohuwa.
Daga cikin shugabannin jam'iyyar da suka tafi zanga-zangar sune shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki; gwamnan jihar Sokoto, AMinu Waziri Tambuwal; shugaban jam'iyyar PDP, Uche Secondus; dan takaran kujeran shugaban kasa, Sule Lamido da shugaban jami'ar Baze University, Datti Baba Ahmed. Kakakin jam'iyyar PDP, Kola Ologbodiyan, ya bayyana hakan ne ta shafinsa na Tuwita a yau Juma'a, 5 ga watan Oktoba, 2018.
Mun kawo muku rahoton cewa Shugabannin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na gudanar da zanga-zanga kan sakamakon zaben jihar Osun da aka kammala kwanan nan na gwamna. Masu zanga-zangan na neman INEC ta kaddamar da dan takarar PDP Ademola Adeleke a matsayin wanda yayi nasara a zaben.

No comments:
Write Comments