Hãdimar Shugaban kasa Muhammadu Buhari na musamman a kafofin watsa labarai ta caccaki Alhaji Atiku Abubakar - Tace lashe tikitin da Atiku yayi zai ba APC sa'a cikin sauki - Onochie tace sai da Atiku siya sannan ya iya ja da abokan takararsa Lauretta Onochie, hadimar Shugaban kasa Muhammadu Buhari na musamman a kafofin watsa labarai ta caccaki Alhaji Atiku Abubakar, bayan ya billo a matsayin wanda zai tsayawa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) takara a zabe mai zuwa. Ta je shafin zumunta, jim kadan bayan kaddamar da sakamakon cewa Atiku ne yayi nasarar samun tikitin takarar jam’iyyar cewa hakan zai basu dama cikin sauki, jaridar Punch ta ruwaito .
NAIJ.com ta tattaro cewa hadimar shugaban kasar tayi ikirarin cewa Atiku ya gudu daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) don guje ma karawa da Buhari a zaben fidda gwani; sannan cewa tsohon mataimakin shugaban kasar yayi gwagwarmayan kafin ya samu tikitin jam’iyyar.

No comments:
Write Comments