Rahotanni sun bayyana, kan yadda aka sayarwa Uba Sani, mai baiwa Gwamnan jihar Kaduna shawara kan harkokin siyasa, tikitin takarar kujerar majalisar dattijai a mazabar Kaduna ta tsakiya a kan $2m.
Wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta, ta zanta da jaridar SaharaReporters a Abuja, a ranar Juma'a, kan wannan badakala.
A cewar majiyar, babbar manajar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta kasa (NPA), Hadiza Bala Usman, ita ce ta cire kudin da hannunta ta baiwa Farouk Adamu. Ya ce, Adamu ya karbi kudin a tsabarsu a Abuja, a madadin Adams Oshiomhole, shugaban jam'iyyar APC na kasa.
SOURCE :HAUSALEGIT.NG
Ya bayyana cewa Uba Sani ya baiwa mataimakin sakataren watsa labarai na APC, Mr Yekini Nabena, kudi har N50m, sai dai Yekini bai karba ba. Majiyar ta yi nuni da cewa, Nabena ya sha fitar da sanarwa kan cewa Shehu Sani ne dan takarar sanata na wannan shiyya, sai dai Nabena ya ce ba shi da ikon bijirewa duk wani mataki da kwamitin gudanar na jam'iyyar za ta dauka.
Sai dai, Hadiza, ta yi barazanar yin duk mai yiyuwa na ganin cewa Shehu Sani bai samu tikitin takarar kujerar sanatan ba, wanda hakan ya yiwa kwamitin gudanarwar jam'iyyar dadi.
Kamar yadda SaharaRepoters ta ruwaito, cewa gazawar duk wani yunkuri na neman hadin kan Nabena kan wannan lamari, ya sa Hadiza ta yanke shawarar bi ta hannun Farouk, wanda shi kuma ya karbi kudin daga wajenta.
Majiyar ta labarta yadda Gwamna El-Rufai ya kwana a ofishin shugaban jam'iyyar na kasa, da kuma barazanar da yayi na goyon bayan Atiku Abubakar, ma damar aka mika sunan Shehu Sani ga hukumar INEC a matsayin dan takarar sanatan mazabar Kaduna ta tsakiya.
Farouk, wanda ya shugabancin kwamitin zaben fitar da gwani na kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar, ya karbi kudin ne ba tare da sanin sauran mambobin kwamitin ba. Mambobin kwamitin sun hada da ministan ilimi, Adamu Adamu; ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika da kuma ministan shari'a, Abubakar Malami.
Wadannan zarge-zarge da suka taru suka yiwa Oshiomhole, na karbar cin hanci da rashawa, ya tilasta babban sakatarensa na watsa labarai, Simon Ebegbulem, fitar da sanarwa a ranar Alhamis, inda Oshiomhole ya yi barazanar daukar mataki ga duk wanda ya kara zargarshi da rashawa.
Sai dai, Nabena ya bukaci Ebegbulem, da ya daina shiga kafofin watsa labarai yana yada farfaganda, tare da tsayawa don fuskantar gaskiyar lamari, kasancewar zargin ya shafi jam'iyyar ne gaba daya.
Wasu daga cikin mambobin kwamitin gudanarwar jam'iyyar na kasa, sun ji dadin yadda gaskiya ta bayyana karara kan irin makudan kudaden da dan takarar ya biya Oshiomhole don sayen tikitin takarar. Wani mamba, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce da yawa daga cikin mambobin sun kosa kan sanin halin da kudaden suke ciki, kasancewar an ware su daga sanin gaskiyar magana tun a farko.
No comments:
Write Comments