Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta kaddamar da cewa barazanar yan siyasa ba zai tsorata ta ba da har zata dagula zaben 2019.
Hukumar ta kuma kaddamar da cewa ta yanke shawarar yin aiki kai-da-kai da yan sanda don tabbatar da zabe na gaskiya da amana.
Da yake Magana a wani taron zantawa da jam’iyyun siyasa wanda hukumar yan sandan jihar Benue ta shirya a Makurdi, kwamishinan zaben na jihar Benue, Dr. Nentawe Yilwatda, ya yi alkawarin cewa hukumar za ta wadatar da dukkanin yan takara da jam’iyyunsu yayin zaben.
Da farko, kwamishinan yan sandan jihar, Mista Ene Okon, ya yi gargadin cewa yan sanda ba za su gaza ba wajen kama duk dan siyasar da suka kama yana karfafa ta’addanci da rikici a lokacin zabe.
Da ya samu wakilcin mataimakin kwamishinan yan sanda, Mista Tunji Akingbola, kwamishinan ya bayyana cewa za su tabbatar da doka da hukunta duk wanda ya take ta.
No comments:
Write Comments