Wani lamari mai kama da wannan ya taba faruwa a jihar, inda wata mata ta kashe mijinta da yaransu uku.
Depunn, mahaifiyar yarinyar, da yanzu haka ke hannun jami'an 'yan sanda, ya kafe kan cewar bai aikata wani laifi ba saboda Allah ne ya umarce shi ya dauki ran jaririyar.
Mutumin, mai matsakaicin shekaru, ya karbo yarinyar daga hannun mahaifiyarta tare da tafiya da ita wani jeji da ke Mbangur a garin Tse-Agberagba, karamar hukumar Konshisha, inda ya shake ta har lahira.
Bayan ya dawo ba yarinyar ne, sai ya shaidawa jama'a, ba tare da wani ya tambaye shi ba, cewar ya cika umarnin Allah a kan yarinyar.
"Mahaifin yarinyar da kansa ya sanar da jama'a cewar ya kashe diyar sa bisa umarnin ubangiji," a cewar majiyar mu.
Wani shaidar gani da ido ya shaidawa majiyar mu cewar Deppun ya amsa laifin da bakinsa, "tunkiya ta ce kuma na sadaukarwa da ubangiji kamar yadda ya umarce ni. Ban taba dora ko hannu a kan dan wani ba, a saboda haka kar wanda ya ga laifina. "
Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Benuwe, DSP Moses Yamu, ya tabbatarwa da majiyar mu cewar sun kama mutumin tare da bayyana cewar suna cigaba da bincike a kansa.
No comments:
Write Comments