Monday

Home Mutumin da ya kashe mahaifiyarsa ya gamu da hukuncin kisa ta mummunar hanya
Majiyar Legit.com ta ruwaito a ranar Litinin 26 ga watan Nuwamba ne Alkalin kotun, mai sharia Daniel Longji ya yanke ma matashi Banchir hukuncin kisan mahaifiyarsa wanda ta haifeshi wai don kawai bata amsa gaisuwarsa.

Da yake karanto hukuncin daya dace da wannan matashi mara Imani, Alkali Daniel yace: “Duba da binciken da kotu tayi game da abubuwan da aka bayyana mata dangane da zarginsa kisan mahaifiyarsa Saratu Banchir da Godwin yayi,
“Kotu ta tabbatar da cewa kai Godwin Banchir ka kashe mahaifiyarka mai suna Saratu Godwin cin rashin Imani da rashin tausayi ba tare da wani dalili ba, don haka na kotu ta yanke maka hukuncin kisa ta hanyar rataya.

“Wannan hukuncin ya zama wajibi ne saboda tanadin da doka tayi ga duk wanda aka kama da laifin kisan kai za’a yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya, don haka hukuncin kotun nan akanka shine za’a ratayeka har sai ka mutu, da fatan ubangiji yayi maka rahama.” Inji shi.S
Tun a ranar 6 ga watan Yuni ne aka shigar da karar Godwin gaban kotun kan tuhumarsa da akeyi da kashe mahaifiyarsa a ranar 21 ga watan Janairu na shekarar 2016 ta hanyar buga mata kotan fatanya.
A cewar Banchir, ya dawo gida ne daga gona a ranar, sai ya tarar da babarsa a zaune a tsakar gida, amma daya gaisheta, sai ta yi banza da shi bata amsa ba, hakan ne ya bata masa rai, inda ya rarumi kotan fatanya ya buga mata har ta mutu.
“Mamata ta dade bata amsa gaisuwana a duk lokacin data dawo daga gona, bata dafa min abinci akan lokaci, tana yawan min fada a duk lokacin da zanyi wanka da ruwan data debo daga rafi, wadannan halayyar da take nuna min suna bata min rai sosai, don haka ne na sa kota na maketa.” Inji shi.

SOURCE : LEGIT.NG 
No comments:
Write Comments