Showing posts with label ta'addanci. Show all posts
Showing posts with label ta'addanci. Show all posts

Monday

Yanzu-yanzu: Yan bindiga sun budewa sabon gwamnan Zamfara wuta

A jiya Lahadi ne, wasu yan bindiga sun budewa motar sabon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, wuta yayinda yake hanyarsa na jajintawa wadanda suka rasa yan uwansu a wani hari da aka kai karamar hukumar Gusau, Premium Times ta bada rahoto.

Masu Idanuwan shaida sun bayyana cewa an budewa motar gwamnan wuta ne da yammacin Lahadi a hanyar garin Lilo.

Majiya ya bayyana cewa Yayinda suka kai harin, yan bindigan sun yi amfani da damar tsayin ciyayi inda suka bude masa wuta.

Ya kara da cewa zuwa yanzu ba'a san yawan wadanda aka rasa ko suka jikkata ba, saboda masu tsaron gwamnan sun yi batakashi da yan bindigan.

KU KARANTA: Yadda Wani dalibi ya kashe kansa a dalilin sabani da budurwarsa.

A rahoton da muka kawo da saifyar yau, mai magana da yawun Sabon gwamnan jahar Zamfara, Bello Matawalle ya bayyaa cewa gwamnan ya jagoranci ayarin jami’an rundunonin tsaro inda suka fantsama cikin dazukan kauyen Wonaka dake garin Gusau da nufin farautar miyagun yan bindiga da suka addabi al’ummar yankin.

Kaakakin, Yusuf Idris ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Lahadi, 2 ga watan Yuni, inda yace gwamnan ya samu rakiyar mataimakin gwamnan jahar, Mahadi Aliyu Gusau, da sauran kwamandojin rundunar tsaro, inda suka fatattaki yan bindigan.

A ranar Asabar, Akalla mutane 8 sun rasa rayukansu yayinda 18 suka jikkata harin da aka kai garin Lilo.

Har ilayau, jihar Zamfara da wasu jihohi basu gushe suna fuskantar barazana daga wajen yan bindiga ba.

SOURCE LEGIT.NG


Buhari ya bada umarnin sakin mutanen Nigeria uku da saudiyya ta kama.

Ciki Harda Daliba Zainab Daga Kano.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci ministan shari'a, Abubakar Malami, da ya tabbatar da cewar hukumomin kasar Saudiyya sun saki matashiyar nan yar Najeriya, Zainab Aliyu, da aka yi kuskuren kama wa bisa zargin laifin safarar kwaya.

Hukumomin kasar Saudiyya sun kama Zainab, daliba a jami'ar Maitama Sule dake Kano, a ranar 26 ga watan Disamba na shekarar 2018 bisa zarginta da shiga da jaka dauke da kwayar 'tramol' zuwa kasar Saudiyya.
Zainab Aliyu
Daliba Zainab Aliyu

Matashiyar ta tashi zuwa kasar Sauddiya daga filin jirgin sama na Mallam Aminu domin gudanar da aikin 'umra' tare da mahaifiyarta, Maryam, da 'yar uwarta, Hajara.

Babbar mai taimaka wa shugaban kasa a bangaren harkokin da suka shafi kasashen waje, Abike Dabiri Erewa, ce ta sanar da umarni da shugaba Buhari ya bayar a ranar Litinin, 29 ga watan Afrilu, ta kara da cewa tuni gwamnatin tarayya ta fara tattauna batun sakin Zainab tare da wasu mutane biyu dake da irin matsalar da Zainab ta samu.

" Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci ministan shari'a ya dauki matakan da suka dace a kan matsalar matashiyar. Mun fara tattauna wa da hukumomin kasa, za ta dawo gida tare da wasu mutane biyu dake da irin wannan matsala," kamar yadda Dabiri ta sanar a shafinta na Tuwita.

DUBA WANNAN: Mutane 5 Masu HAtsari a Duniya Da Ake Nemansu Ruwa a Jallo. 

Mahaifin Zainab ne ya fara rubuta wata takardar korafi da ya aika wa hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) a kan zargin cewar an saka kwaya a jakar diyar sa.

Daga bisani, binciken NDLEA ya gano cewar akwai gungun wasu ma'aikan kamfanonin jirgin sama da suka kware wajen yin cushen kwayoyi a jakankunan matafiya.

Thursday

Soyayya batayi rana ba : Rikicin masoya ya Aika wani saurayi har lahira.

Wani matashi dan shekara 29 dake aikin tuka kwale-kwale a jahar Bayelsa, Alabo Enai ya hallaka kansa sakamakon bakin ciki daya turnukeshi bayan samun wani dan sabani tsakaninsa da budurwarsa Blessing.
Rikicin masoya, nishadin masoya

Majiyarmu ta ruwaito matashi Alabo dan haifaffen karamar hukumar Brass a jahar Bayelsa sun samu matsala ne da budurwarsa Blessing yar kabilar Ologbobiri a karamar hukumar Ijaw ta kudu, wanda hakan ta kai ga alakarsu tana tangal-tangal.

KU KARANTA: Radadin Talauci : Wani mutum ya bankawa kansa wuta...   

Duk kokarin da matashin saurayin yayi na shawo kan budurwarsa yaci tura, wanda hakan yayi sanadiyyar kashe kansa inda yayi amfani da ragar kama kifi ya daure wuyarsa daga saman bishiya, ma'ana dai ya rataye kansa, abin mamaki kuma wannan budurwa Blessing ce ta gano gawarsa a rataye.

Wani ganau ya bayyana cewa "Cikin kankanin lokaci jama"a suka taru suna kallon gawar matashin, sun mamakin dalilin da yasa ya hallaka kansa, ga shi kuma bai bar wani sako ko wata wasika ba, badurwar ta bayyana cewa sun samu matsala da saurayin nata watakila hakan ne yasa ya aikita wannan danyen hukunci.

Ita ma budurwa tayi karin haske kamar haka “Matsalar da ta faru tsakanin mu itace na fada masa ina son zan koma garinmu a kudancin Ijaw, shi kuma ya nuna bai amince da hakan ba, amma da na fahimci ranshi ya baci sai na hakura muka cigaba da zama tare, a wannan ranar daya mutu sai da nace masa yazo mu tafi wasan Easter, amma sai yaki, yace na tafi kawai.”

MAJIYA LEGIT.NG

Tuesday

Radadin Talauci : Wani mutum ya bankawa kansa wuta...

An garzaya da Nweze zuwa asibitin koyar wa na jami'ar Alex Ekwueme da ke Abakaliki domin ceto rayuwar sa bayan ya banka wa kansa wuta a bayan ajin makarantar firamare ta St. Patrik da ke unguwar Kpirikpiri, a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi.

Talauci, ya kona kansa

Rahotanni sun bayyana cewar Nweze ya daure kafafunsa kafin ya cinna wa kansa wuta.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ebonyi, Lovett Odah, ya ce suna binciken lamarin domin tabbatar da gaskiyar cewar kashe kansa ya yi.

Ana saura kwana daya ya aikata hakan, Nweze, dan asalin garin Umuogharu a karamar hukumar Ezza ta Arewa, ya yiwa makobtansa korafin cewar ya gaji da rayuwar fatara da rashi da suka sa ko ciyar da kansa ba ya iya yi.

DUBA WANNAN: Yadda ake mayar da hakora suyi haske ƙal-ƙal a cikin awa daya  

A cewar kakakin rundunar 'yan sandan; " mun gaggauta aika motar daukan masu bukatar taimakon gagga wa zuwa wurin da abin ya faru bayan mun samu kira daga wani mutum.

" Yanzu haka muna kan gudanar da bincike a kan lamarin, ba mu samu isassun bayanan da zasu tabbatar mana da cewar kashe kansa ya yi ba, ko kuma wani abu ne daban ya faru ba ."

MAJIYA : LEGIT. NG

Friday

Zalunci: Shugaban Makaranta ya kone wata 'Daliba kurmus bayan ta tona masa asiri

Mutuwar wannan budurwa mai shekaru 19 kacal a duniya, Nusrat Jahan Rafi, ya haifar da mummunar zanga-zanga a yankin kasar dake nahiyyar Kudancin Asia. Firai Ministan kasar, Sheikh Hasina ya sha alwashin hukunta dukkanin masu hannu cikin wannan zalunci.
tearcher burned his student in Bangladesh
Bayan da masu hannu cikin wannan muguwar aika-aika sun gaza samun biyan bukata yayin da suka nemi Nusrat ta janye korafin keta mata haddi, sun yi mata wanka da makamashi na Kalanzir kuma suka kone kurmus.


Hukumar 'yan sanda yayin karin haske dangane da wannan lamari na takaici ta bayyana cewa, ta samu nasarar cafke mutane 17 ababen zargi inda daya daga cikin su ya amsa laifi sa da cewa sun aikata hakan ne bisa umurni na shugaban makaranta.

Babban jami'in dan sanda mai gudanar da bincike a kan wannan mugun ji da mugun gani, Muhammad Iqbal, ya shaidawa manema labarai na jaridar AFP cewa, Nusrat ta riga mu gidan gaskiya a ranar 10 ga watan Afrilu inda ba ta gushe ba wajen ci gaba da bayyana koke a kan shugaban makarantar da ya keta mata haddi.

KARANTA KUMA: Hattara! : "Yan ta'addar jihar zamfara sun fara kaura suna shiga wasu jahohi.

Jagorar kungiyar kare hakkin bil Adama ta kasar, Meenakshi Ganguly, yayin babatu na neman a tabbatar da yiwa Nusrat adalci tare da nema mata hakki, ta kuma bayyana yadda gwamnatin kasar Bangladesh ta gaza ta fuskar kare al'umma daga cin zarafi.

SOURCE LEGIT. NG

Hattara! : "Yan ta'addar jihar zamfara sun fara kaura suna shiga wasu jahohi.

A ranar Alhamis dinnan ne da ta gabata, gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola, ya bukaci jami'an tsaro da sarakunan gargajiya da su lura sannan kuma su dakile duk wani shiri na 'yan ta'addar jihar Zamfara, wadanda suke yin kaura daga jihar suna komawa wasu jihohi.

zamfara killings, kashekashen zamfara

Hakan ya biyo bayan sanarwar da babban sakatarensa a fannin sadarwa ya fitar, Mista Adeniyi Adesina, bayan gwamnan ya yi magana a wurin wani taro, akan gudanar da tsarin tsaro, wanda sarakunan gargajiya, shugabannin hukumomin tsaro, kungiyoyin jama'a, 'yan siyasa, 'yan kasuwa da sauransu suka hallata a Osogbo.


Oyetola ya ce "ya zama wajibi a sanya matakan da za su magance matsalar 'yan ta'adda da ke faruwa a jihar Zamfara shigowa jihar Osun."
Gwamnan ya jaddada bukatar tabbatar da tsaro ta hanyar tattara bayanai, sannan sarakunan gargajiya su saka ido a yankunansu da kuma bukatar a fadakar da jami'an tsaro su sanya ido wurin dakile duk wani shiri na ta'addanci a jihar.

Gwamnan da kuma jami'an tsaro sun gargadi masu bada gidajen haya, akan bai wa mutane wadanda ba su da kyakkyawar masaniya a kansu.

KU KARANTA: A karon farko an yiwa wasu birai dashen kwakwalwar Dan-Adam.
"Idan ka bawa mutumin da baka san shi ba hayar gida, kuma muka gano cewa dan ta'adda ne, to duk abinda ya biyo baya kai ka jawowa kan ka," in ji Oyetola.

Ya bukaci sarakunan gargajiya da su yi aiki tukuru, domin masu hakar ma'adanai suna nan suna yawo a wasu yankuna na cikin jihar.

Gwamnatin tarayya ta hana hakar ma'adanai a jihar Zamfara, bayan ta samu bayanan cewa 'yan ta'addar jihar su na da alaka da masu hakar ma'adanai wadanda ba su da lasisi.

SOURCE LEGIT.NG

Thursday

Jerin mutanen da sojoji suka kashe yayin kai hari akan "yan ta'adda ; Cewar Sarakunan zamfara

A jiya Laraba, 17 ga watan Afrilu, majalisar sarakunan Zamfara sun saki jerin sunayen mutanen garin da harin ya kashe su 11 yayinda aka kaiwa yan bindiga harin a karamar hukumar Zurmi.
zamfara killings

Sunayen sune:

Mai Daji Barau,

Na Dumburum,

Suwaiba Alka,

Yar Guru Na Dumburum,

Maryam Shafiu,

Dahe Malan Sule,

Buhari Dan Kurma,

Zaliha na Dumburum,

Aisha Akilu,

Alamin Alka

Fati ‘Yar Gum.

A cewar sarakunan, wasu mutane 11 sun samu raunuka sakamakon wadannan hare-hare a garin Dumburum, karamar hukumar Zurmi na jihar ranar 9 ga watan Afrilu, 2019.
Sunayen wadanda suka samu raunukan sune:

Haruna Kusu,

Muhammad M Sani,

AbdulRazak Abubakar,

Yakubu Yunusa,

Dan Diyya,

Sa’a Dayyabu,

Yar’wargi Mamman,

Gwamna na Dumburum,

Rashida Alka,

Maryam Akilu

Sadiq Sukuranu.

KARANTA WANNAN : Babu Batun cire tallafin mai a Najeriya - NNPC ta magantu 

Kana sun ambaci cewa akwai mutane 20 da aka harin ya rusawa muhalli.
A hira da manema labarai da suka gabatar a Gusau, Wakilin sarakunan jihar, Sarkin Fulanin Bungudu, Alh Hassan Attahiru ya jaddada cewa hari sojin ya kashe al'ummar gari.

SOURCE LEGTI.NG