Da yake amsa tambaya a kan irin shawarar da zai bawa 'yan siyasar Najeriya, Shehun Malamin ya shawarci 'yan takara su saka bukatar kasa a gaba a cikin manufofinsu na yakin zabe.
Da aka tambayi Sheikh Gumi ko mai zai ce a kan shawarar da shugaba Buhari ya bawa malaman addini a kan su nesanta kansu daga harkokin siyasa domin kare mutuncinsu, sai ya kada baki ya ce,
"a'a, abinda yake son fadi a fakaice shine malaman addinin Islama da Kirista su daina sukar sa. Idan ba zamu yaudari kan mu ba, mun san cewar malaman addini mutane ne kamar kowa kuma suna da bukatu kamar yadda ragowar jama'a keda su; suna son ganin an samu shugabanni nagari da zasu taimaki al'umma bakidaya. Na san tabbas akwai malaman dake fakewa da addini domin biyan bukatar kansu, amma akwai wadanda kishin kasa ne a gabansu.
Sai dai, ya ce gwamnatin Buhari na yaudarar jama'a ne kawai da batun yaki da cin hanci bayan a zahiri sun mayar da yin arziki a lokacin mulkinsu laifi.
Kazalika ya soki gwamnati a kan cigaba da tsare shugaban mabiya mazahabar Shi'a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, da kuma artabu da nagoya bayansa dake zanga-zangar neman sakinsa, yana mai bayyan cewar mabiya Shi'a 'yan kasa ne kamar kowa dake da hakkin yin addininsu kamar kowa.
No comments:
Write Comments