YADDA ZA KA DUBA SUNAN KA DA MAZABAR KA A ONLINE .
Yau saura kwanaki 2 kacal wa'adin da hukumar zaben Najeriya INEC ta bayar na kowane mai son yin za6e a 2019 ya garzaya maza6ar da yayi rajista domin tabbatar da sunan sa. Tare kuma da kai korafin sa a cibiyar mazabar sa (ward center) idan bai ga sunan sa ba, ko kuma akwai matsala a sunan na sa.
GA DAMA TA SAMU !
Idan ba ka da iko na zuwa mazabar ka domin duba sunan ka, to za ka iya amfani da wayar ka domin duba sunan ka.Ga yadda abin ya ke :
HANYA TA FARKO
1 - bude manhajar ka ta Opera ko UC Browser sai ka yi bincike ta Google a wannan adireshin :Voters.inecnigeria.org
Akwai bayanan katin zaben ka da za a nemi ka cike a wannan shafi :
i- sunan jihar ka,
ii- sunan mahaifin ka,
iii- sunan ka,
iv- kwanan watan haihuwar ka (date of birth).
MISALI :
i- KANO
ii- MUHAMMAD
iii- IBRAHIM
iv- 01-10-2000.
KO KUMA :
(i) sunan jihar ka,
(ii) sunan ka (First name),
(iii) lambobi biyar NA KARSHEN VIN ( Voter's Identification Number ) da ke a cikin katin zaben ka, (kana kuma iya sa su gabaki daya).
Sannan ka aika.
MISALI :
i - KANO
ii - IBRAHIM
iii- 01234.
HANYA TA BIYU
2 - ka aika da sunan # Jihar ka, da # Sunan ka, da kuma lambobi 5 na kashe a VIN naka dake a cikin katin zaben ka zuwa ga WANNAN LAMBA :20120, ko kuma: 08171646879.
MISALI :
KANO
IBRAHIM
01234
zuwa ga 20120, ko 08171646879.
Allah Ya bada sa'a.
A TUNA CEWA KATIN ZABEN KA SHI NE MAKAMIN KA WAJEN FATATTAKAR DUK SHUGABAN BA YA KYAUTATA MAKA, TARE DA ZABEN WANDA KAKE SO YA SHUGABANCE KA.
Allah Ya yi mana zabi mafi alheri. Ameen.
No comments:
Write Comments