Wednesday

Home Yankin arewa maso gabas za ta marawa Buhari baya a 2019 : Kungiyar kamfen
Shugaban kungiyar kamfen din shugaban kasa Muhammadu Buhari na Next Level, Honourable Umar Waziri Kumo, ya bayyana cewa mutanen yankin arewa maso gabas za su marawa Buhari baya kwansu da kwarkwatansu don ganin yayi nasara a zabe mai zuwa. Yace hakan zai kasance ne saboda tarin ci gaba da gwamnatinsa ta kawo a rayuwarsu.

Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Talata, 25 ga watan Disamba bayan wani ganawa da yan siyasa da matasan yankin wanda aka gudanar a Riveredge Hotel, Bauchi, Kumo, wanda hadimi ne na musamman ga shugaban kasar yayi ikirarin cewa gwamnatin tarayya tayi kokari sosai a yankin kama daga gina hanyoyi wanda ya hade dukkanin jihohin yankin shida da kuma yaki da ta’addanci inda yak are rayuka da dukiyoyin jama’a.

A cewarsa, harkar noma wanda shine babban aikin da mutanen yankin ke yi ya samu ci gaba sosai sakamakon jajircewar gwamnatin APC
.

“Wannan hujja ce an habbaka noman shinkafa da sauran kayayyakin abinci wanda yasa Najeriya ta zamo mai dogaro da kai wajen abinci."
Ya nuna yakinin cewa dan takarar shugaban kasa a APC zai kawo dukkanin yankin arewa maso gabas a zabe mai zuwa.

SOURCE LEGIT.NG
No comments:
Write Comments