Wasu tsoffin yan bindigan Niger Delta sun kai mamaya mashigin majalisar dokokin kasar inda suka bukaci a biyasu alawus dinsu sannan suka nemai a dakatar da shugaban shirin bayar da tallafi ga tubabun yan bindiga, Birgediya Janar Paul Boroh (mai rtitaya).
Tsoffin yan bindigar sun kasance dake da kwalaye da rubutu irinsu, Ya Zama Dole Dokubo Ya Tafi sannan A Biya Mu Hakkinmu.
Masu zanga-zangan sun iso kofar majalisar dokokin ne yayinda majalisar ke shirin tarban shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda zai gabatar da kasafin kudin 2019.
Yayinda aka shirya gabatar da kasafin kudin da mislain karfe 11 na safe, masu zanga-zangan sun isa kofar majalisa tun karfe 7:30 na safe.
Tsoffin yan bindigan sunce sun yi zanga-zangan ne domin janyo hankalin shugaban kasa akan ta’adin da ake yi a shirin.
No comments:
Write Comments