Jam'iyar nan ta Action Alliance ta fara gudanar da kamfe dinta a kananam hukumomin jihar Imo a ranar Litinin dan yada manufar shugaban kasa Muhammad Buhari.
A yayin gudanar da wannan gangami a Okwe dake karamar hukumar Onuimo jam'iyar tace "Buhari yaci zabe ya gama".
Dan takarar gwamna a jam'iyar ta AA Uche Nwosu da dan takarar sanata Ndubuisi Emenike da dantakarar majalisar jihar ta Imo Simeon Iwenzu sun bayyana cewa Buhari yanada goyan baya a jihar.
Yan takarar sun ara da cewa banda Buhari jihar jam'iyar AA kadai zasu zaba.
Jam'iyyar AA ta Imo, ta fara aikin ganin shugaba Buhari ya zarce a wannan watan
Nwosu ya bayyana cewa " yana da tabbacin shugaban kasa Muhammad Buhari zaici zaben da zai gudana a ranar 16 ga watan Fabrairu,ku zabi Muhammad Buhari a jam'iyar APC sannan ku zabi ragowar yan takarar dake jam'iyar AA".
"Zanyi aiki tukuru tamkar matashi sannan zan bada gudummawa sosai a bangaren noma zan kuma goyawa mutanen Onuimo bisa ga noman shinkafa" .
Jam'iyyar AA ta Imo, ta fara aikin ganin shugaba Buhari ya zarce a wannan watan
"Jam'iyar AA zata samar da ilimi kyauta a jihar Imo,zamu bada magani kyauta tun daga kan jinjiri zuwa dan shekara Bakwai,da kuma tsofaffi yan shekara 75 zuwa sama"
Dan takarar gwamnan ya kara fargar da mutane dasu kula matuka sannan ya shawarci matasa da mata dasu kula dasu kula da kuri'un su.
Nwosu yace "Karku bari su bata zaben,ku tabbatar da masu kula da akwatunan Ku ne suka irga kuri'un ku saboda wannan zabe yana da matukar muhimmanci a dimukradiyar mu,ku zabi jam'iyar AA sannan ku kiyaye ".
No comments:
Write Comments