Saturday

Home › › An kãma wasu masu satar yara a Kano.
An kama wasu da ake zargin masu satar yara ne a wasu unguwanni biyu da ke jihar Kano.



-Wata mace daya daga cikin wadanda ake zargi an samu wasu makudan kudi a asusun ajiyar bankinta da ake zargin kudin yaran da ta sayar ne Dubun wasu masu Satar mutane a Kano ta cika Dubun wasu masu satar yara ta cika da Allah Ya taimaka suka shiga hannun jami'an 'yan sanda a jihar Kano.

An sace kananan yara kimanin 13 a unguwannin Walalambe da Hotoro da har yanzu babu labarinsu.
Wadanda aka kame ake kuma zarginsu da satar wata yarinya ce budurwa da kuma wani magidanci wadanda ba bayyana sunayensu ba.

A cewar wani rahoton gidan Rediyo mai zaman kansa cikin shirin In da ranka ya ce, masu satar kananan yaran wasu gungun mutane ne wadanda ke bayar da kudi ga wasu matasa ana satar musu yaran.

Kuma a cewarsa, budurwar da ake zargi wacce kuma ta ke hannun 'yan sanda ta sace wani yaro ne mai suna Sadiq a lokacin da dubunta ya cika. Bugu da kari a lokacin da aka tsananta bincike a kanta, an gano wasu makudan kudade a cikin asusun ajiyarta na banki wanda iyayen gidanta ke aiko mata idan ta kai musu yaran. Rahoton ya cigaba da cewa, 'yan sanda sun kama wani mutum wanda shine ke sa wannan budurwa tana sato masa yaran.

A Kwanakin baya al'ummar yankin Hotoro na karamar hukumar Tarauni da kuma Walalambe na karamar hukumar Gezawa duk a jihar, sun shiga rudani a sakamakona yawaitar batar kananan yara a yankunansu. Abin da kamar wasa har ta kai an sace yara sama da 13 cikin kankanin lokaci wanda hakan ya sa suka garzaya fadar Sarkin Kano suna kukan a kawo musu dauki a shekarar 2016 da ta gabata.

Wannan magana ta tayar da hankalin iyaye musamman wadanda aka sacewa yaran, da farkon fitowar maganar sai aka dauki labarin kamar tatsuniya ce domin ana ganin satar yara kamar magana ce ta almara. Dangane da wannan lamari wasu mutanen a jihar na fargabar cewa, wannan wani babban aiki ne da ya taso, tare da tambayar ko za a yi hukuncin da ya dace kan batun, da kuma sanar da al'umma irin binciken da ake yi.

Domin a kwanan baya a unguwar Kawo Lambu da ke karamar hukumar Nassarawa mazauna unguwar sun taba kama wata mata mai harkar bori da ba da maganin gargajiya da wasu yara kanana a gidanta, amma da aka kai wa maganar gaba babu abin da aka yi a kai.



©facebook/HAUSAPOST28
No comments:
Write Comments