Tuesday

Home Ainihin abin da ya sa Sarkin Yakin Atiku yake shirin barin Jam'iyyar PDP
Darekta Janar na yakin neman zaben Atiku Abubakar a jam’iyyar PDP watau Gbenga Daniel, ya sanar da cewa yayi murabus daga tafiyar jam’iyyar adawa ta PDP, kuma ya ajiye siyasa a gefe guda.

Labarai da dumi dumi


Sahara Reporters ta bi diddiki ta kawo dalilan da ake gani, su ne su ka tunzura tsohon gwamnan ya tsere daga jam’iyyar ta PDP. Gbenga Daniel yana ganin cewa ba a damawa da shi a PDP tun da Atiku ya samu tikin takarar 2019.

Daga cikin abubuwan da su ka Gbenga Daniel ya fice daga PDP akwai hana sa kujerar shugaban jam’iyya da aka yi. Daniel yana cikin wadanda su kayi harin shugaban PDP, wanda a karshe aka dauke ta kaf daga kasar Yarbawa.

KU KARANTA: Ka san duk magudin da APC ke shirya wa, PDP ta kafa hujja da kalaman Buhari.

Gbenga Daniel shi ne yayi wa Atiku Abubakar yakin samun tikitin shugaban kasa a PDP, amma ana zargin cewa PDP ta maida Gbenga Daniel saniyar ware bayan Atiku ya samu takara inda aka maye gurbin sa da Bukola Saraki.

Rikicin PDP tsakanin Obasanjo-Kashamu, da kuma rigimar Kashamu da Adebutu a Ogun yana cikin abin da ya sa tsohon gwamnan ya fice daga jam’iyyar. Wannan rikici dai ya jawowa PDP matolsala a jihar a zaben 2019 ana ji ana gani.

Tsohon gwamnan na Ogun, Gbenga Daniel yana ganin cewa akwai wani boyayyen shiri da ake yi na kauda Yarbawa daga cikin jam’iyyar PDP. Babu mamaki hakan ya sa ya tattara ya bar jam’iyyar.
No comments:
Write Comments