A yayin da lamuran tsaro a jiahr Zamfara ke kara tabarbarewa, mazauna yankunan karamar hukumar Tsafe sun koma neman asirin tsarin kai daga wurin mafarauta da ragowas masana surkullen gargajiya.
A wata kasuwa da ke kauyen Tsauni mai nisan kilomita 35 daga Tsafe, an ga jama'a na bin dogon layi domin gana wa da masana jeji da surkulle domin karbar asirin da zai kare su idan 'yan bindiga su kawo masu hari.
Mazauna kauyukan na neman magani ko asirin da zai hana bindiga tasiri a kan su.
Ko a kwanakin baya sai da gwamna jihar Zamfara, Aldulaziz Yari, ya bayyana cewar 'yan bindigar da ke kai hare-hare a jihar sun fi jami'an tsaron Najeriya makamai na zamani.
'Yan bindiga na cigaba da kai hare-hare tare da yin garkuwa da mutane a sassan jihar Zamfara, musamman a yankin da ake hakar zinare.
Ko a cikin makon da mu ka yi bankwana da shi sai da Legit.ng ta kawo maku labarin cewar wasu 'yan bindiga sun sace wani likita, Mista Jeng Sunail, dan asalin kasar Koriya ta Arewa da ke aiki da babban asibitin karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.
Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ce ta sanar da hakan a cikin wani jawabi da kakakin ta, DSP Shehu Mohammed, ya fitar.
A cewar jawabin, abokin aikin likitan ne mai suna Dakta Li Dung ya sanar da rundunar 'yan sanda labarin sace likitan ta hannun ofishinta da ke karamar hukumar Tsafe.
Wani mazaunin yankin ya shaidawa majiyar mu cewar wasu 'yan bindiga ne suka kutsa rukunin gidajen ma'aikatan asibitin da misalin karfe 9:00 na daren ranar Litinin inda su ka wuce kai tsaye zuwa gidan Sunail tare da yin awon gaba da shi zuwa wurin da babu wanda ya sani.
Batun satar mutane tare da garkuwa da su na neman zama ruwan dare a jihar Zamfara, har yanzu kokarin gwamnati na shawo kan lamarin bai hana 'yan bindiga a jihar cigaba da karen su da babu babbaka ba.
SOURCE LEGIT.NG

No comments:
Write Comments