Monday

Home Zaben gwamna: APC ta lashe jahohi 10, PDP ta samu nasara a jahohi 8
Duk da yake ba’a kammala tattara dukkanin alkalumman sakamakon zaben gwamnonin Najeriya daya gudana a karshen makon daya gabata ba, amma zuwa yanzu hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, ta sanar da wasu jahohin.
kano result, bbc result, abba gida gida, ganduje ya fadi
According To BBC

Majiyar Legit.ng ta ruwaito zuwa yanzu manya jam’iyyun siyasar Najeriya da kuma yan takarkarunsu sun san matsayinsu a wadannan jahohi da aka kammala sanar da sakamakonsu, inda a yanzu haka APC ke kan gaba da jahohi 13, yayin da PDP ke bi mata da jahohi 7.

KU KARANTA: INEC ta bayyana yadda za ta fitar da wanda ya yi nasara a Kano

Daga cikin jahohin da jam’iyyar APC ta samu nasara sun hada da Legas, Gombe, Kwara, Kebbi, Nassarawa, Yobe, Neja, Katsina, Ogun, Jigawa, Kaduna, Borno da Zamfara, yayin da PDP ta dauke jahohin Abia, Cross Rivers, Delta, Ebonyi, Enugu, Oyo da Akwa Ibom, kamar yadda INEC ta sanar.
Ga dai sunayen yan takarar da suka lashe zaben jihohinsu da kuri’un da suka samu kamar haka;
APC
Legas, Babatunde Sanwo Olu 739, 445
Kwara, Abdulrahman Abdulrasaq 331, 546
Kebbi, Atiku Bagudu 673, 717
Jigawa, Muhammad Abubakar Badaru 810, 993
Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya 364, 179
Neja, Abubakar Sani Bello 526,412
Katsina, Aminu Bello Masari 1, 178, 864
Nassarawa, Abdullahi Sule 327, 229
Yobe, Mai Mala Buni 444, 013
Ogun, Dapo Abioudun 241, 670
Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai 1,045,417
Zamfara, Mukhtar Shehu 534,541
Borno, Babagana Zulum 1,175,440
PDP
Oyo, Seyi Makinde 515, 621
Enugu, Ifeanyi Uguwanyi 449, 935
Akwa Ibom, Emmanuel Udom 519, 712
Ebonyi, David Umahi 393, 043
Abia, Okezie Ikpeazu 261, 127
Cross Rivers Ben Ayade 381,484
Delta Ifeanyi Okowa 925,272
Zuwa yanzu ana dakon kammala aikin tattara sakamakon zabe a jihohin Kano, da Borno, yayin da hukumar zabe tace zabe bai kammala a jihohin Filato, Sakkwato, Adamawa da Bauchi ba.
No comments:
Write Comments