Monday

Home An nemi Buhari ya cire tallafin man fetur ko kuma ya ga ba daidai ba
A yayin da tattalin arzikin kasar nan Najeriya ke ci gaba da tabarbarewa, kasar ta batar da kimanin Naira Tiriliyan goma wajen bayar da tallafi na shigo da man fetur a tsakanin shekarar 2006 zuwa 2018.
Kamar yadda jaridar vanguard ta ruwaito, wata kungiyar zamantakewa masaniyar tattalin arziki ta BudgIT, ta ce Najeriya ba za ta fidda kanta zuwa ga tudun tsira ba matukar za ta ci gaba da kasancewa a zamani na biyan tallafin man fetur.

Baba buhari

Ka cire tallafin man fetur domin ci gaban Najeriya - BudgIT ta shawarci Buhari
BudgIT cikin wata sanarwa da sa hannun babban jami'in ta, Shakir Akorede, ta ce binciken da ta gudanar a kwana-kwanan nan ya tabbatar da cewa ci gaba da dorewar Najeriya a zamani na biyan tallafin man fetur zai dawwamar da ita cikin mafi kuncin rayuwa fiye da sauran kasashen duniya na bakar fata.

Kungiyar ta ce ba ya ga haifar da ababe masu tasiri zuwa ga rashawa, biyan kudin tallafin man fetur ya kan haifar da bambamce-bambamce na farashin sa da hakan ya ke kasancewa mawuyacin hali ga gwamnati wajen daidaita farashi a kasa.

KARANTA KUMA: Shugaban Kasar Aljeriya Ya Yi Murabus Bayan Muguwar Zanga-zanga.

A yayin da ake sa ran adadin al'ummar Najeriya ya kai kimanin miliyan 398 zuwa shekarar 2050, gwamnati ba za ta iya ci gaba da daukar nauyin kasar ba ta fuskar batar da dukiya wajen tabbatuwar ci gaban ta da inganta rayuwar al'umma.

BudgIT na ci gaba da shawartar shugaban kasa Muhammadu Buhari akan gaggauta cire tallafin man fetur domin bunkasa muhimman bangarori na sufuri, makamashi, lafiya da kuma uwa uba ilimi da ya kasance babban tubali kuma ginshiki na ci gaba.
No comments:
Write Comments