Sunday

Home Shugaba Buhari ya Nuna Takaicinsa game da rikicin taraba da Adamawa.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana takaicinsa a akan rikicin da ya addabi kabilar Jukun da Tibi a jihar Taraba da kuma na Fulani da Genjon da kuma kabilar Bachama na jihar Adamawa abin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da kuma jikkata dubbai.
bacin ran buhari, buhari angry, buhari ya bata rai

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne ta bakin mai bashi shawara a kan harkokin watsa labarai, Malam Garba Shehu, a sanarwar da ya bawa manema labarai a birnin Abuja jiya Asabar.
Ya ce, ”Tashin hankali da zubar da jini ta kowanne hanya abu ne da ba za a amince da shi ba ta kowanne hanya, musamman a wannna lokacin da ake bukukuwan Ista a fadin kasar nan, duk kuwa dimbin darussa da wannna lokacin ke koya mana na zaman lafiya da juna ba tare da nuna bambamci ba.
”Tashin hankali ba zai taba zama hanyar maganin rashin fahintar da muke fuskanta ba a tsakanin mu na mutane.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kuma yi kira da a gagauta kawo karshen rikicin tare da samar zama lafiya a fadin jihohi gaba daya.

Ya ce, gwamnati za ta nemi a tattauna a tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki don gano musabbabin rikicin don kawo karshen rikicin gaba daya.”

DUBA KUMA : Dadin Kowa Sabon salo Episode 102 - Daga Arewa24 TV  

Haka kuma shugaban kasar ya bukaci Malaman addini su gaggauta samar da hadin kai da zaman lafiya a tsakanin dukkan bangarorin dake tashin hankali a jihar filato da Kaduna da Taraba da kuma Adamawa.

Shugaban kasa Buhari ya kuma umarci hukumar NEMA da sauran kungiyoyin bayar da agaji su kai dauki ga mutanen dake fuskantar matsananciyar matsaloli a sakamokn rikicin.
”Shugaba Buhari ya kuma bukaci gaggauta samar da sojoji a yankunan don samar da zama lafiya cickin gaggawa.

SOURCE LEADERSHIP.NG
No comments:
Write Comments