Assalamu'alaikum Barkan mu da yau, Da fatan kowa lafiya.
Ayau muna ɗauke da cikakken bayani aka Yadda ake connecting na xender ta wayar android zuwa computer ta hanyar wifi, wannan hanya tanada mauƙar sauri wajen tura files zuwa kan computer ko kuma turawa daga computer zuwa kan waya, a wannan zamani cigaba yazo matuƙa sakamakon idan kukayi duba zuwa shekarun suka gabata ana amfani da bluetooth ne wajen transper na files daga wannan wayar zuwa wannan wayar, a yanzu kuma cigaba yazo ida ake amfani da Xender wadda tafi bluetooth sauri nesa ba kusa ba, idan kuka biyo wannan rubutu namu a yanzu zaku laƙanci yadda ake connecting na android xender da kowacce irin computer, wannan yana aiki akan kowacce waya matuƙar dai android ce.
Aika files ta amfani da wannan hanyar yana da matuƙar sauki da kuma saurin aiki.
Mene yasa zanyi amafani da wannan hayar don kawai tura files zuwa computer?
- Yana iya kasancewa USB naka ya lalace.
- Wayarka ta android bata iya connecting da computer.
- Kana son Tura Large files kamar Bidiyoyi ko kuma Games masu Nauyi.
- Ko kuma dai kawai kanason gawadawa don Gaba.
Abubuwan da ake buƙata sune :
- - Wayar Android , Application na Xender a cikin wayarku ta Android
- - Computer , Chrome, firefox ko opera ko kuma duk wata browser mai ƙarfi a cikin coputer ku.
Step 1.
Ku buɗe xender Application na cikin wayarku ta Android, sai ku taɓa icon na option wanda yake a sama daga ɓangaren hagu, (duba hoton ƙasa).
Step 2.
Bayan kun taɓa wannan icon na option, Da zarar ya buɗe zakuga inda aka saka Connect to PC, kamar yadda kuke gani a hoton ƙasa.
Step 3.
Bayan kun taɓa Connect to PC , waje na gaba zai buɗe , anan zakuga option guda biyu, akwai WEB CONNECT akwai HOT SPOT, to ku Zabi Hot spot kamar yadda kuke gani a hoton ƙasa, sai ku taɓa CREATE HOT SPOT , zaku ganshi daga kasa. (duba hoton kasa)
Step 4.
Bayan kun taɓa create hot spot, zai fara loading bazai ɗauki lokaci ba , cikin ƴan sakanni zai nuno muku wasu Lambobi, kamar yadda kuke gani a hoton ƙasa.
Sai ku kwafi Wannan lambobin ku rubutasu dai-dai a address bar na browser ta computer ku, kamar yadda kuke gani a hoton ƙasa.
Kuna dannawa zai fara loading , cikin ƴan sakanni zakuga wayar ku ta android tayi motsi (ba motsin jiki ba), To sai ku taba Accept, kamar haka⤵⤵⤵
Shikenan A yanzu kunyi connect na Android da Computer ta hanyar Amfani da Xender Application, Yanzu mun gama bayani akan yadda ake connect ,sai bayani akan Yadda Zaku tura files tsakanin computer zuwa waya ko daga wayarku zuwa computer, sai ku biyo mu.
YADDA AKE TURA FILES DAGA COMPUTER ZUWA A WAYA TA HANYAR AMFANI DA XENDER.
Bayan kun gama da gabaɗaya waɗancan matakan na sama wato yadda ake connect, bayan komai yayi connected to a lura, za'ayi amfani da computer ne wajen aikin walau tura files zuwa waya ne ne ko kuma tura files daga waya zuwa computer ne , to duka da computer zaku yi, waya kuwa sai dai ku ajiyeta a gefe kuma.
Ku biyo waɗannan matakan don sanin yadda ake turawa.⤵⤵⤵
Step 1.
Bayan komai yayi connected, idan kuka duba screenshoot na ƙasa zakuga inda aka sa UPLOAD MUSIC , to wannan button na upload shine zai baku damar aikawa da files zuwa wayarku ta Android wadda ku ka ajiye a gefe.Step 2.
A wannan hoton na ƙasa kuma zakuga inda aka saka alamar DOWNLOAD, wato daga gefen Upload Button, to wannan Download button shine zai baku damar turo files daga wayarku dake ajiye a gefe zuwa computer.
DUBA WANNAN KUMA.
- Yadda Ake Dawo da Lambar WhatsApp Idan ta Daina Aiki
- Yadda zaku maida lambar wayar ku zuwa ta kasashen waje. in 5min
- Yadda Zaku Bude Facebook Account Ba Tare Da Suna Ba.
- Yanda Zaka Samu Rancen Kudi Har N100,000 A Layin Etisalat New(9mobile)
- Yadda Ake Connecting Na Android Xender Da Computer. : Android Tutorial 2020.
Ko kuma Ku ziyarci Page namu mai tâken YADDA AKE....🔗🔗
Bayani Akan Sabon Starin Startup Nigeria Program 2019 https://t.co/h1MwKnPSwG https://t.co/h1MwKnPSwG June 14, 2019 at 01:21AM— AREWASOUND (@Arewasound) June 14, 2019
No comments:
Write Comments