Sunday

Home Yadda Gidauniyar Sheikh Gumi ta bawa Kwankwaso kyautar iya jagoranci
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, da tsohon gwamnan jihar Zamfara, Ibrahim Wakala, da ragowar wasu mutane uku sun samu kyautar karrama wa ta musamman da gidauniyar Sheikh Gumi ke bayar wa ga shugabannin da suka nuna halaye nagari duk shekara.


Ragowar mutane uku da aka karrama tare da Kwankwao da Wakala sune; Farfesa Abdulmumin Hassan Rafindadi, Kanal Yawale Iliyasu (mai ritaya) da Dakta Muhammed Suleiman Adam, babban limami a masallacin Sultan Bello kuma lakcara a jami'ar jihar Kaduna.

Da yake mika kyautar gare su yayin rufe Tafsirin azumin wanna shekarar, Dakta Ahmad Gumi, dan marigayi Abubakar Gumi, ya ce ana bayar da kyautar ne ga jagororin da suka nuna kware wa a mulki da kuma wadanda suka nuna kwazo a bangaren yada ilimi.

Ya ce sanata Rabi'u Kwankwaso, wanda Injiniya Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida) ya wakilta a wurin taron, ya samu kyautar ne saboda gudunmawar da ya bawa bangaren ilimi lokacin da yake gwamna a jihar Kano.

DUBA WANNAN: Babban Dalilin da yasa sarki sunusi II bai halarci rantsuwar Ganduje ba.

Gumi ya kara da cewa gidauniyar ta karrama Wakala saboda kasancewar sa malamin addinin da ya shiga harkokin siyasa har ta kai ga ya rike matsayin mataimakin gwamna.

A nasu bangaren, wadanda aka bawa kyaututtukan sun nuna jin dadinsu tare da mika godiya da gidauniyar marigayi Sheikh Gumi.

SOURCE LEGIT.NG

No comments:
Write Comments