Sunday

Home Gwamna Matawalle Na Zamfara Zai Kaddamar Da Aikin Filin Jirgin Sama
Sabon Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya bayyana cewa cikin kwana 100 na mulkinsa aikin zai fara gudana akan shirin gina filin jirgin sama na Gusau. Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin da ya kai wata ziyara a wurin da ake shirin kaddamar da filin jirgin saman a ranar Asabar da ta wuce.

A wata sanarwa da mai taimakawa gwamnan kan kafafen watsa labarai ya sanyawa hannu, Mallam Yusuf Idris, ya bayyana cewa gwamnan ya ce kaddamar da wannan filin jirgin saman zai kawo wa jihar ci gaba tare da kuma bude kofofin samar da ayyukan yi a jihar.

Ya ce; gwamnatin za ta mai da hankali wajen bunkasa tattalina arzikin jihar, tare da fito da hanyoyin da za su bunkasa kudaden harajin da jihar ke samar wa.
Ya ci gaba da cewa; gwamnan ya yi alkawarin maishe da jihar ta bunkasa ta fuskancin tattalin arziki da zamantakewa, inda ya yi kira ga masu kudi da su zo su zuba hannu jari a jihar.

Har wala yau sanarwar ta ce gwamnan ya kai ziyara Otel din Gusau, inda ya tarar da yadda Otel din ya lalace. Inda ya nuna takaicinsa na yadda ya tarar da ku san kowanne sashe na jihar yadda ya lalace, ya yi alkawarin gyara su tare da inganta su.

Shi dai wannan filin jirgin saman, an fara kaddamar da shi ne tun shekara goma da ta wuce a lokacin mulkin gwamna Mamuda Shinkafi.
No comments:
Write Comments