Monday

Home Yanzu-yanzu: Kotun zabe ta yi watsi da bukatar Atiku da PDP na duba na'urara zabe na INEC
Kotun shari'ar zabe shugaban kasa ta yi watsi da bukatar jam'iyyar Peoples Democratic (PDP) da dan takararta, Atiku Abubakar, na duba na'urar hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta INEC.

A hukuncin, kwamitin alkalai biyar sun yi ittifakin cewa ba zai yiwu a amsa bukatar PDP ba saboda an kai ruwa rana kan shin hukumar INEC ta yi amfani da yanar gizo wajen tattara sakamakon zaben shugaban kasa. Channels TV ta bada rahoton cewa alkalan sun bayyana cewa ba zai yiwu sun sanya baki cikin al'amarin ba a wannan lokaci.

KARANTA KUMA : Amurka ta kai wa Iran hari, ta lalata musu makaman yaki  

 Lauyan Atiku da PDP, Levy Uzokwu, ya bukaci kotun zaben ya wajabtawa INEC ta basu daman bincike cikin yanar gizo da na'urar 'Card Reader' da akayi amfani da su lokacin zabe. Amma lauyan INEC, Yunus Usman, ya bukaci kotu tayi watsi da wannan bukata inda yace: "Suna tambayarmu mu basu abinda bamu da shi,"

Ya kara da jawo hankalin kotun da bukatar da PDP ta gabatar ranar 6 ga Maris cewa kayyayakin zabe kawai ta bukaci gani ba yanar gizo ba Jam'iyyar PDP da Atiku Abubakar na kalubalantar nasarar shugaba Muhammadu Buhari na APC a zaben shugaban kasan da ya gudana ranar 23 ga Febrairu, 2019.

SOURCE LEGIT.NG
No comments:
Write Comments